26.3 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

ASUU: Yajin aiki ya mayar da wani dalibin karatun likitanci zama mai sayar da abinci a jihar sokoto

IlimiASUU: Yajin aiki ya mayar da wani dalibin karatun likitanci zama mai sayar da abinci a jihar sokoto
public.jpeg

Tsawaita yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi ya mayar da Usman Abubakar-Rimi, dalibin karatun likitanci a jami’ar Usman Danfodiyo ta Sokoto (UDUS) dan kasuwa.

Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a yau Juma’a a Sokoto, Abubakar-Rimi ya ce ya zama mai sayar da abinci don rayuwa mai inganci a dalilin yajin aiki da malaman jami’o’in gwamnati ke yi wanda hakan sanya dalibai zama a gida.

Wata biyu kenan da ya fara sayar da abinci,wanda ya ke alfahari da mallakar wurin sayar da abinci a cikin birnin Sakkwato, ya ce yajin aikin da ASUU ta yi shine ya ba shi damar fara sana’ar.

“Na dauki hayar shago, inda na dauki ma’aikata takwas masu sarrafa shayi da dafa Indomie, ina sayar da kayan sha na kwalba da gwangwani, masara, shinkafa,farfesu da kuma wuri cire kudi POS.

“Ana sayar da filet daya na abinci daga N200 zuwa sama.”
Abubakar-Rimi kuma ya mallaki wani shago akan titin Fodio shima a cikin birnin Sokoto inda yake siyar da kayan mata, hula, jakunkunan dalibai, da takalma.

“A koyaushe ina farin cikin ganin cewa na zama dan kasuwa saboda a halin yanzu na ɗauki mutane 10 a shaguna na biyu.
“Ina saro kwai da kaji daga manyan gonaki a saukin kuɗi, “Idan na zama Likita, ina so in yi aiki a wurin da ba zai dinga cinye min lokaci ba saboda a halin yanzu, na fara daina sha’awan aikin albashi.

Ina so in kafa kantin sai da magani, in yi aiki a asibiti mai zaman kansa sannan in tsunduma cikin wasu kamfanoni masu zaman kansu da suka dace da sana’ata,” Abubakar-Rimi ya bayyana.

Dalibin na shekarar karshe a karatun likitanci ya shawarci ɗalibai da su yi amfani da wannan lokacin da kyau kuma su shiga kasuwanci.

Ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya waiwayo wannan yajin aiki da akeyi inda ya yi kira ga malaman da suma su yi la’akari da radadin da dalibai suke ciki, su sasanta da gwamnatin tarayya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe