24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Jimamin mutuwa: Naira Marley yayi zanen fuskar sarauniyar Ingila a hannun sa

LabaraiJimamin mutuwa: Naira Marley yayi zanen fuskar sarauniyar Ingila a hannun sa

Shahararren mawaƙin nan na Kudancin Najeriya, Azeez Adeshina Fashola wanda akafi sani da Naira Marley, yayi ta’aziyyar rasuwar sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II.

Naira Marley ya garzaya shafukan sada zumunta inda ya nuna sabon zanen da akayi masa a jikin sa domin nuna girmamawa ga sarauniyar ta Ingila wacce ta riga mu gidan gaskiya. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.

Ana cigaba da jimamin mutuwar sarauniyar Ingila

Sarauniyar ta Ingila ta mutu ne a ranar Alhamis, bayan ciwon ta yayi tsanani a ranar Alhamis.

A halin da ake ciki dai a yanzu mutanen ƙasar Birtaniya da na duniya na cigaba da juyayin mutuwar sarauniyar wacce tafi kowa daɗewa a kan kujerar masarautar Birtaniya.


Mutane da dama daga sassa daban-daban na duniya sun yi jimamin mutuwar sarauniyar ta Ingila wacce ta mutu tana da shekaru 96 a duniya.

Naira Marley ya nuna irin tasa hanyar jimamin mutuwar sarauniyar

Domin nuna irin na sa jimamin mutuwar ta sarauniyar, Naira Marley, ya sanya anyi masa zanen fuskarta a hannun sa.

Naira Marley wanda a da yake rayuwa a ƙasar ta Birtaniya kafin dawowar sa Najeriya, ya sanya wani bidiyo inda ya nuna hoton zanen da akayi masa na fuskar sarauniyar.

Ya sanya bidiyon ne dai a manhajar Instagram a ranar Alhamis sa’o’i kaɗan bayan an sanar da mutuwar sarauniyar.

A cikin bidiyon Naira Marley yayi addua ga sarauniyar wacce ta rigamu gidan gaskiya.

Yadda aka shirya liyafar auren wasu kwaɗi a Indiya

A wani labarin na daban kuma, wani ƙauye a ƙasar Indiya ya shirya liyafar shagalin bikin auren wasu kwaɗi.

An shirya liyafar auren wasu kwaɗi a wani ƙauye a ƙasar Indiya. Lamarin ya auku ne a wani ƙauye dake cikin jihar Assam a ƙasar ta Indiya.

An dai shirya auren ne domin neman samun ruwan sama da ake fama da ƙarancin sa a jihar ta Assam. An dai kwashe makonni a jihar ana fama da matsanancin zafi da fari. Jaridar Al-jazeera ta rahoto.

Jihar ta Assam na shan fama da matsalolin fari da kuma ambaliyar ruwa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com


Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe