32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Jami’an kwastam sun kama buhunhuna 16 makil da mazakutar jakai guda 7,000 ana shirin shillawa da su China

LabaraiJami’an kwastam sun kama buhunhuna 16 makil da mazakutar jakai guda 7,000 ana shirin shillawa da su China

Jami’an hukumar kwastam sun yi ram da mazakutar jakai guda dubu bakwai, 7,000 da ake shirin yin sumogal din su zuwa Hong Kong, kasar China a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Jihar Legas, LIB ta ruwaito.

Shugaban kwastam din yankin, Sambo Dangaladima, wanda ya bayyana buhunhuna cike da mazakutar jakunan ya shaida yadda masu su su ka biya kudin da za a wuce da su kimanin N216,212,813.

A cewar Dangaladima, warin da buhununan ke yi ne ya janyo hankulan jami’an. Ya cigaba da cewa:

Masu kokarin fitar da su sun ce mazakutar shanaye ne. Amma bayan duba su dakyau aka gane cewa na jakai ne.

Wannan ne karo na farko da muka taba kwace wani abu mai kama da hakan. Ba za mu yarda ana irin wannan sana’ar a gabanmu ba.”

Hukumar kwastam ta samu nasarar kwace katan 383 na maganin kara karfin maza yayin jima’i iri-iri

Hukumar kwastam mai dakile fasakwabrin kayayyaki a Najeriya ta bayyana yadda ta kama maganin tari na codeine wanda yakai darajar naira miliyan 212 da kuma maganin karin kuzarin ga namiji yayin saduwa BBC Hausa ta ruwaito.

Hammi Swomen, shugaban hukumar kwastam na yankin Apapa da ke jihar Legas, ya ce sun kama kwantena dauke da katan guda 2,875 na maganin tarin da kuma kanta guda 383 na kwayoyin dake kara wa maza kuzari yayin saduwa, wadanda aka bayyana sunayen su daban-daban.

Haka zalika, an samu katan guda 99 na injin mai nima abubuwa daban-daban a cikin kwantenar.

“Mun samu bayani akan yadda aka dauko flas din abinci, amma kamar yadda kike gani ya bayyana abubuwa ne da suka bambanta gaba daya,” a cewarsa.

Ya cigaba da bayyana cewa “wannan ba kage bane, kawai an shigo da haramtattun kaya ne”.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe