23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda aka shirya liyafar auren wasu kwaɗi a Indiya

LabaraiAl'adaYadda aka shirya liyafar auren wasu kwaɗi a Indiya

An shirya liyafar auren wasu kwaɗi a wani ƙauye a ƙasar Indiya. Lamarin ya auku ne a wani ƙauye dake cikin jihar Assam a ƙasar ta Indiya.

An dai shirya auren ne domin neman samun ruwan sama da ake fama da ƙarancin sa a jihar ta Assam. An dai kwashe makonni a jihar ana fama da matsanancin zafi da fari. Jaridar Al-jazeera ta rahoto.

Jihar ta Assam na shan fama da matsalolin fari da kuma ambaliyar ruwa.

Dalilin shirya bikin auren

Mashiryin auren Deepak Das ya bayyana cewa:

Manoma na fama da matsaloli sosai sakamakon farin da ake yi, hakan ya sanya mu ka shirya wannan auren

Ana barin kwaɗin su more auren su

Bayan an kammala shagalin bikin ana sakin kwaɗin domin su je su more amarcin su.

Muna yi musu wanka ɗaya bayan ɗaya, sannan bayan an kammala abubuwan al’ada, sai mu kai su majami’a mu kewaya da su, daga nan sai mu sake su zuwa cikin ruwa.

Cewar Cheena Bora, wacce ta halarci bikin

Wannan dai ba shine karon farko da ake gudanar da bikin na kwaɗi ba a yankin, sai dai auren na su ba kowane lokaci yake cika daɗewa ba.

A shekarar 2019, wani ƙauye ya raba auren wasu kwaɗi da akayi bayan an samu ambaliyar ruwa.

Abin al’ajabi: Masallacin da ya kwashe shekaru a nutse cikin tafki ya bayyana a Indiya

A wani labarin na daban kuma, wani masallaci ya bayyana bayan ya kwashe shekaruna nutse a ƙasar Indiya.

A cewar wani rahoton Kashmir Media Service, shekara talatin da suka gabata, wani masallaci ya nutse a cikin ruwan dam ɗin Phulwaria, a gundumar Nawada cikin jihar Bihar ta ƙasar Indiya.

Sai dai bayan shekara talatin da nutsewar masallacin a cikin dam ɗin, a yanzu masallacin ya bayyana.

Masallacin ya nutse ne a ƙauyen Chiraila a tsahin Rajauli saboda ruwan da yake shiga cikin ɓangaren Kudu na dam ɗin.

A shekarar 1985, masallacin wanda aka sani da Noori Masjid ya nutse a Phulwaria Dam, masallacin yana da tsawon kafa talatin daga ƙasa zuwa rufin sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe