24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Abin al’ajabi: Masallacin da ya kwashe shekaru a nutse cikin tafki ya bayyana a Indiya

LabaraiAbin al'ajabi: Masallacin da ya kwashe shekaru a nutse cikin tafki ya bayyana a Indiya

A cewar wani rahoton Kashmir Media Service, shekara talatin da suka gabata, wani masallaci ya nutse a cikin ruwan dam ɗin Phulwaria, a gundumar Nawada cikin jihar Bihar ta ƙasar Indiya.

Sai dai bayan shekara talatin da nutsewar masallacin a cikin dam ɗin, a yanzu masallacin ya bayyana.

Masallacin ya nutse ne a ƙauyen Chiraila a tsahin Rajauli saboda ruwan da yake shiga cikin ɓangaren Kudu na dam ɗin. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

A shekarar 1985, masallacin wanda aka sani da Noori Masjid ya nutse a Phulwaria Dam, masallacin yana da tsawon kafa talatin daga ƙasa zuwa rufin sa.

Ginin sa bai yi komai ba

A cewar rahoton matasa da yawa sun garzaya wurin domin ganewa idon su masallacin bayan ya bayyana.

Ba su taɓa tunanin cewa akwai masallacin a wurin ba domin su kawai a iya sanin su ruwa kawai suke gani.

A lokacin da mutane suka shiga ciki, sun ga cewa babu abinda ya samu ginin masallacin. Abin lura anan shine duk da masallacin ya kasance a nutse cikin ruwa har na tsawon shekara talatin, tsarin ginin sa bai lalace ba.

Masallacin ya daɗe a wurin

An yi amanna cewa masallacin ya kasance a wurin tun ƙafin a fara gina dam ɗin Phulwaria a shekarar 1979.

Duk da kammala ginin dam ɗin, masallacin bai yi komai ba. Sai dai gabaɗaya harabar yankin ciki har da masallacin sun nutse a cikin ruwan dam ɗin.

Haka kuma anyi amanna cewa an gina masallacin ne a farkon ƙarni na 20 sannan yana da kusan kimanin shekara 120 yanzu. An cimma wannan ƙiyasin ne bisa la’akari da yanayin ginin masallacin wanda ya ɗararwa sauran gine-gine na lokacin Mughal.

Wata budurwa mai rawar TikTok a masallaci ta faɗa komar ƴan sanda

A wani labarin na daban kuma ƴan sanda sun cafke wata budurwa mai rawar TikTok a masallaci.

Ƴan sanda a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan sun cafke wata budurwa mai amfani da manhajar TikTok bisa laifin tiƙar rawa a masallaci.

An kama budurwar ne tare da ƴan tawagarta a ranar Litinin bayan bidiyonta tana rawa a masallacin Faisal ya ƙaraɗe shafukan sada zumunta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe