28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Yara uku ne suka mutu sakamakon wani gini da ya fado a Jigawa

LabaraiLabaran DuniyaYara uku ne suka mutu sakamakon wani gini da ya fado a Jigawa
hhh

Yara uku ne suka mutu sakamakon wani gini da ya rufta a ranar Alhamis a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sanadiyyan ruwan sama da akayi kamar da bakin kwarya, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta bayyana.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Adam, ya ce ginin ya ruguje ne a unguwar Jigawar tsarki sakamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama anayi a daren Laraba.

‘Yan sanda sun bayyana sunayen wadanda harin ya rutsa da su Farida Idris ‘yar shekara 6 Mariya Idris ‘yar shekara 3 da kuma Bilkisu Yahya ‘yar shekara daya da wata shida dukkansu a kauyen ‘Yakasai Jigawar Tsada’ da ke yankin karamar hukumar Dutse.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wadanda harin ya rutsa da su sun mutu nan take kafin a ceto su.

“Bayan samun rahoton ne jami’an tsaro suka zarce inda abin ya faru, suka kwashe gawarwakin aka garzaya da su babban asibitin Dutse.

“Da isowarsu, Likitan da ke bakin aiki ya ba da shaida cewa sun mutu. An dauki hoton gawarwakin sannan aka mika wa ’yan uwansu don yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Kwamishanan ‘yan sanda reshen jihar Jigawa, Aliyu Tafida, ya jajantawa iyaye, ‘yan uwa da addu’ar Allah Ta’ala ya ba su kwarin guiwar jure wannan rashi, in ji sanarwar ‘yan sandan.

Lamarin ya biyo bayan mutuwar mata hudu da wani jariri dan watanni bakwai a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guri ta jihar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe