32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Mun samu makamai irin na sojoji tare makudan kudaden kasashe daban-daban a gida da ofishin Mamu, DSS

LabaraiMun samu makamai irin na sojoji tare makudan kudaden kasashe daban-daban a gida da ofishin Mamu, DSS

Rundunar jami’an tsaro masu fararen kaya, DSS ta bayyana wa duniya abubuwan da ta gani a gida da ofishin Tukur Mamu, mamallakin jaridar Desert Herald.

Dama LIB ta bayyana cewa Mamu hadimin babban malamin addinin nan ne, Ahmed Gumi, wanda ya dade yana shiga cikin sasanci da kuma cinikin kudin fansa har ta kai ga an saki fasinjojin jirgin kasan Kaduna wadanda aka kama a watan Maris din 2022.

Sannan an kama Mamu a filin jirgin kasa da kasa na Kano bayan dawowarsa daga Masar inda jami’an tsaro su ka kama shi yana hanyarsa ta zuwa Saudiyya don yin umara.

Kakakin DSS, Peter Afunanya, a wata takarda da ya saki a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba, ya ce an samu abubuwan zargi a gidan Mamu da ofishinsa bayan sun je bincike.

Kamar yadda ya bayyana a takardar:

“Yanzu haka, jami’an tsaro sun kammala binciken gida da ofishin Mamu bayan an ba su damar yin hakan.

“Yayin binciken, an ga abubuwan zargi ciki har da makamai irin na sojoji. Sannan an samu kudade na kasashe daban-daban tare da alamar cinikayya ta makudan kudade.

“Yayin da za a ci gaba da bincike akansa, tabbas sai Mamu ya tsaya gaban kotu.”

Harin Jirgin kasan Kaduna- Abuja: An kama Tukur Mamu a Misra

Malam Tukur Mamu, mutumin da ya jagoranci ciniki tsakanin ‘yan uwan fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, da ‘yan bindiga a watan Maris ya shiga hannun ‘yan sanda a Cairo, babban birnin Misra tare da iyalansa, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda manema labarai su ka tabbatar, gwamnatin Najeriya ce ta sa a kama Mamu, wanda shi ne mai jaridar Desert Herald. An kama shi a babban filin jirgin sama na Cairo inda ya kwashe awanni 24 a hannun jami’an tsaron kasancewar yana kan hanyarsa ta zuwa umara sannan aka maido da shi Najeriya.

Yayin tattaunawa da manema labarai, Mamu ya ce ya bar Najeriya ne a ranar Talata bayan jami’an tsaron Egypt sun gama caje shi ba tare da ganin wani abin zargi tare da shi ba.

Mamu ya bayyana cewa ya gano shirin gwamnatin Najeriya na kama shi a wata kasa kamar yadda aka yi wa mai rajin kafa kasar Yarabawa, Sunday Igboho, amma hakan ba zai yuwu a Egypt ba saboda gwamnatin kasar ta ga duk takardunsa ingantattu ne.

Idan ba a manta ba, Mamu ne ya tsaya wurin cinikin kudin fansa da ‘yan bindiga, sannan ya yi zargin gwamnatin Najeriya tana barazana da rayuwarsa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe