27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Bayan fadi darasinsa, dalibai 11 sun daure malamin lissafi jikin bishiya, sun lakada masa dukan tsiya

LabaraiBayan fadi darasinsa, dalibai 11 sun daure malamin lissafi jikin bishiya, sun lakada masa dukan tsiya

Rundunar ‘yan sanda ta ruwaito yadda dalibai 11 su ka taru wurin daure malamin lissafinsu jikin bishiya tare da zane masa jikinsa, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Sai da su ka ja shi zuwa harabar marakantar da sunan za su tattauna da shi dangane da wata jarabawar da ya basu har su ka fadi.

Daga nan ne su ka kama malamin, Suman Kumar, bayan ya bayyana musu makin da su ka ci a shafin yanar gizon makarantar, Soneram Chaure, sannan su ka daure shi jikin bishiyar tare da zane shi.

Bidiyoyi da hotunan yadda lamarin ya auku sun bazu a shafukan sada zumunta inda kowa yaga yadda aka zane mutumin.

Kamar yadda odditycentral.com ta ruwaito, bincike ya bayyana yadda daliban su ke a fusace inda daya daga cikinsu ya nuna dukan da malamin yayi masa bayan ya fadi darasin har da bandeji a kansa.

Dalibai 11 cikin 32 da ke ajin ne su ka fadi warwas a jarabawar kamar yadda indiatimes.com ta nuna.

Wannan lamari ya hassala kusan dalibai 200 inda su ka dinga zanga-zanga a tsakar makarantar.

Daliban makarantar Jharkhand ne da ke kauyen Dumka su ke da alhakin yin wannan aika-aikar ga malaminsu.

Wani dan sanda ya bayyana cewa:

“Mun samu bayani akan yadda lamarin ya auku sannan mun tattauna da malaman makarantar. Mun gano cewa kananun maki aka ba su sannan malamin ya gaza yi musu bayani dangane da yadda aka yi hakan ta faru.”

Malamin da aka daka, Suman Kumar a wata tattaunawa da ANI tayi da shi ya ce:

Daliban sun kiramu da suna za su zauna da mu sakamakon jarabawarsu bata yi kyau ba. Kuma hakan na da alaka da makin da aka ba su, kuma shugaban makarantar ne ke da wannan alhakin.”

Shugaban ofishin ‘yan sandan Gopikandar, Nityanand Bhoka ya sanar da manema labarai cewa makarantar bata kai korafin daliban ba saboda gudun bacin sunayensu.

Sai daga baya ne malamin da kansa ya kai wa hukumar kara.

Ana zargin jami’an DSS da lakada wa Ali Artwork (Madagwal) bakin duka tare da azabtar da shi

Shafin Kannywood na manhajar Facebook ta saki wata budaddiyar wasika ga shugaban hukumar ‘yan sanda masu farin kaya, DSS.

Kamar yadda wasikar ta bayyana yadda Ali Artwork yayi bidiyon wayar da kai akan ta’addanci wanda hakan yasa wasu suke bibiyar rayuwarsa da ta dan uwansa.

An bayyana yadda dan uwan Alin yake rai a hannun Allah, kuma ko da Ali ya kai wa jami’an korafi tun ranar 9 ga watan Yunin 2022, ba a dauki mataki ba ya ci gaba da zuwa yana neman daukinsu.

Yau da ya koma wurinsu ne su ka zane shi tare da azabtar da shi ta hanyar sanya shi ya kalli rana. Da wannan dalilin ne ake neman daukin shugaban hukumar, Alhaji Magaji Yusuf Bichi, da ya taimaka ya yi adalci a lamarin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe