27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Dalilan da yasa aka haramta waƙar ‘Warr’ ta Ado Gwanja

LabaraiKannywoodDalilan da yasa aka haramta waƙar 'Warr' ta Ado Gwanja

Gwamnatin Najeriya ta haramta waƙar nan ta ‘Warr’ ta shahararren mawaƙin nan Ado Gwanja wacce yayi a baya-bayan nan.

Sanarwar haramcin waƙar ta ‘Warr’ ya biyo ta hannun hukumar kula da kafafen sadarwa ta Najeriya, NBC. BBC Hausa ta rahoto.

A sanarwar da hukumar ta NBC ta fitar ta bayyana cewa waƙar ‘Warr’ ta bayyana rashin tarbiyya da kalaman da ba su kamata ba.

Dalilan haramta waƙar ‘Warr’

NBC ta ce ”a cikin waƙar akwai zagi kai tsaye da kuma nuna yadda wasu ke tangadi bayan sun yi mankas da giya.”

Wasu baituka daga waƙar waɗanda zagi ne ƙarara a cikin su a cewar hukumar, sune kamar haka:

”….Kafin a san mu ai mun ci kashin Ubanmu…

”…Zani zo bari in shafa hoda, ko kin zo da ke da hodar ku ubanku zan ci, warr…

”…Kowa yace zai hana mu uban sa zan ci…

Baya ga kalaman da hukumar ta ce sun saɓa doka, NBC ta ce a bidiyon waƙar ta ‘Warr’ wacce yanzu haka take tashe a shafukan sada zumunta da kuma manhajar Youtube, an kuma nuna yadda ake shan giya muraran.

A cewar NBC hakan ya saɓa sashen doka na 3.18.2, da kuma na 3.9 na hukumar kula da kafafen sadarwa ta Najeriya.

Haka kuma hukumar NBC ta koka kan yadda wasu gidajen rediyo da talabijin a Arewacin Najeriya ke cigaba da yaɗa waƙa, inda take tunanin cewa kafofin ba su saurari waƙar sun fahimce ta da kyau ba kafin sanya ta a idon duniya.

Waƙoƙin ‘Warr’ da ‘Chass’ na Ado Gwanja, na kwana-kwanan nan sun jawo cece-kuce sosai daga malamai da masu sa ido kan lamurran yau da kullum.

Sai dai waƙokin sun yi fice sosai a wurin matasa a Arewacin Najeriya.

Finafinan Hausa basa ɓata tarbiyya dama can yaranku basu da tarbiyya -Nafisa Abdullahi

A wani labarin na daban kuma, Nafisa Abdullahi ta soki masu cewa finafinan Hausa na ɓata tarbiyyar yara.

Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar finafinan Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kalamai masu kaushi akan mutanen dake sukar finafinan Hausa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe