27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda uku a jihar Enugu

LabaraiWasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda uku a jihar Enugu
Neja: Wani jami'in 'yan sanda ya rasu bayan sun halaka ‘yan bindiga da dama yayin harin da suka kai wani gini

Jami’an ‘yan sanda uku ne aka kashe a daren Laraba a lokacin da ‘yan bindiga suka kai wani hari a New Haven, karamar hukumar Enugu ta Arewa a jihar Enugu, a kudu maso gabashin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:15 na dare a tashar bas

An ce ‘yan bindigan sun bude wa jami’an wuta, inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi.

Lamarin ya haifar da fargaba ga mazauna yankin.

Wani ganau, wanda ke da shagon daukan hoto kusa da wurin da lamarin ya faru, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigar sun auka wa jami’an ‘yan sandan ne.

“’Yan sanda uku ne an kashe, amma gawarwaki biyu kawai muka gani. Sun ce an kai daya asibiti,” inji shi.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES faruwar lamarin a safiyar Alhamis.

Ya ce jami’an na aikin sintiri ne a lokacin da ‘yan bindigar suka zo cikin wata mota kirar Lexus SUV suka far musu.
“An tabbatar da mutuwar jami’an su uku a asibiti,” in ji shi.

Mista Ndukwe, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce an fara farautar wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe