24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Rikicin Cikin Gida: Ya kamata maza su rika taya matan su girki, da rainon yara

LabaraiAl'adaRikicin Cikin Gida: Ya kamata maza su rika taya matan su girki, da rainon yara

A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Yaki da Cin Hanci da Jama’a ta Jihar Legas (DSVA) ta bukaci maza da su rika taimaka wa matan su da ayyukan gida.

Sakatariyar Zartaswa, ta DSVA, Lola Vivour-Adeniyi, itace ta ba da wannan shawarar a Katagowa Market, yayin da take ba da shawarwari kan Jima’i da Jinsi (SGBV), mai taken: “Men Wey Sabi”.

“Wasu matan suna mutu ne saboda ba su yi wa mazajensu girki ba, wasu matan kuma ana cin zarafinsu ne saboda ba sa iya biyan bukatun mazajen su.

“A yau muna kokarin ganin maza sun sa hannu a ayyukan cikin gida cikin; kamar su girki; tsaftace gida; da chanza pampas; wanda wannan ayyuka ana ganin su a matsayin aikin mata ne.

“Ba raini ba ne dan ka taya matar ka aikin gida.

A cewarta, yana da kyau a sauya tsarin zamantakewa ta hanyar karya ra’ayin jinsi wanda ke dada karuwa, kai tsaye ko a kaikaice, laifin cin zarafin jima’i da kuma jinsi.

Matashi ya makala wayar wuta jikin kofar gidansu don ta ja samarin da ke zuwa hira wurin kanninsa
Wani matashi dan kasar Ghana ya zake wurin bayar da kariya ga kanninsa mata daga mazan da ke zuwa wurinsu da dare, Yen.com.gh ta ruwaito.

A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, matashin ya bayyana yadda wutar lantarki za ta ja duk wani bakon da ya kawo ziyara har ya kai ga taba kofar gidansu, musamman samarin da ke kai wa kanninsa farmaki.

Bidiyon ya dauki hankalin mutane da dama inda wasu su ke ganin cewa ya kai makura wurin kare kanninsa, ababen kaunarsa.

Shafin todaysblog9ja ne ya wallafa bidiyon wanda mutane da dama su ka dinga tsokaci iri-iri, wasu su na yaba masa yayin da wasu su ke kusarsa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe