Wata ‘yar Najeriya mai amfani da suna itzeimzi ta bayyana a kafar TikTok inda ta bayyana yadda kitso ya ke kawo mata makudan kudade a Ottawa, kasar Canada, Legit.ng ta ruwaito.
A guntun bidiyon wanda ta wallafa, ta ce a rana daya tana samun $600 wato N255,450. A dayan bidiyon ta ce ta samu $200 wato N85,150 har da $50 wato N21,287.50 yayin da ta kitsa wa wata gashinta.
Har ila yau, ta wallafa bidiyonta a tsakar titin Canada don mutane su tabbatar da cewa a kasar take.
‘Yan Najeriya sun bazama bangaren tsokaci inda su ka dinga tambayoyi yayin da wasu su ke ta fadin ra’ayoyonsu dangane da sana’ar.
A lokacin da aka dauki wannan rahoton, mutane da dama sun yi tsokaci.
michealsundayezec yace:
“Sai mutane su dinga kirga kudi ba tare da duba harajin da take bayarwa ba ko kuma kudin da take siyayyar kayan bukatunta ba.”
mihzzguddy tace:
“Kai! Amma ina na Najeriya ina asarar fasaha.”
obinnasam82 yace:
“Shin ana iya biyan mai koyo irin wannan kudin?, sai ta amsa shi da cewa: “Ni nayi wannan da dalibi na ba.”
‘Yar Najeriya ta bayyana bidiyonta tare dattijon baturen da ke shirin yin wuff da ita
Wani bidiyo mai ban sha’awa yana ta yawo a kafafen sada zumunta na wata bakar fata da bature wadanda suka hadu da juna a karon farko, Legit.ng ta ruwaito.
Masoyan sun hadu ne ta kafar sada zumunta har suka fara soyayya. Bayan shekaru 3 da suka kwashe sai suka ga dacewar su hadu da juna.
Baturen ya zo har Najeriya don ganinta a karon farko, daga nan ne suka dauki wani bidiyo mai ban sha’awa wanda ya kayatar da mutane da dama.
A bidiyon wanda shafin Yabaleftonline ya saki, sun tsaya kusa da juna yayin da suka rungume juna suna murmushi.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com