Ƴan sanda a jihar Neja sun cafke wani matashi Umar Shehu, mai shekara 31 a duniya bisa laifin safarar makamai ga ƴan bindiga da ƴan ta’adda a jihohin Neja, Kaduna da Katsina.
Jaridar Daily Trust ta ambato kakakin hukumar, Wasiu Abiodun, a cikin wata sanarwa na cewa, Shehu wanda ɗan asalin Bakori ne a jihar Katsina, an cafke shine a kwanar Dikko cikin ƙaramar hukumar Gurara.
Abiodun yace wanda ake zargin ya amsa cewa ya kai wa ƴan ta’adda makamai a dajin Madaki, jihar Katsina; sansanin Ganai a dajin Maidaro, jihar Kaduna; da kuma wani ɗan ta’adda a yankin Kwamba/Maje a Suleja.
Matashin ya amsa laifin sa
Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa ya siyo makamai a hannun wani Abdulmani daga jihar Taraba, wanda tawagar rundunar FIB ta halaka a Kaduna a farkon shekarar nan, inda yace yana samun N100,000 akan dukkanin alburusai 500 da ya kai kowane sansanin ƴan bindiga.
An cafke wani matashi mai ba ƴan bindiga bayanai
Haka kuma ƴan sanda a jihar sun cafke wani matashi, Nasiru Musa, mai shekara 30 a duniya, wanda ake zargin yana ba ƴan bindiga bayanai waɗanda suka addabi Tegina a ƙaramar hukumar Rafi.
Abiodun yace matashin da ake zargin an cafke shi tare da wasu mutum shida, yana da hannu a cikin sace wasu mutum huɗu da halaka biyu daga cikin su a Tegina.
Matashin da ake zargin wanda yace ya samu N200,000 daga cikin aikin ta’addancin, yace yana shirin sace shugaban ƙaramar hukumar Rafi kafin a kama shi.
Ƴan sanda sun kama wani tsohon soja da yake safarar makamai ga ‘Yan ta’adda a jihar Zamfara
A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun cafke wani tsohon soja mai safarar makamo ga ƴan ta’adda a jihar Zamfara.
Jami’an ƴan sanda a jihar Zamfara, sun kama wani tsohon soja kuma fitaccen dan fashi da ya ke kai wa ƴan ta’adda makamai a yankin Arewa maso Yamma.
Wanda ake zargin, mai suna Sa’idu Lawal, an ce ya dade yana ta’addanci ga al’ummar jihohin Neja, Kaduna, Katsina, da kuma Kebbi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com