23 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Matashi ya makala wayar wuta jikin kofar gidansu don ta ja samarin da ke zuwa hira wurin kanninsa

LabaraiMatashi ya makala wayar wuta jikin kofar gidansu don ta ja samarin da ke zuwa hira wurin kanninsa

Wani matashi dan kasar Ghana ya zake wurin bayar da kariya ga kanninsa mata daga mazan da ke zuwa wurinsu da dare, Yen.com.gh ta ruwaito.

A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, matashin ya bayyana yadda wutar lantarki za ta ja duk wani bakon da ya kawo ziyara har ya kai ga taba kofar gidansu, musamman samarin da ke kai wa kanninsa farmaki.

Bidiyon ya dauki hankalin mutane da dama inda wasu su ke ganin cewa ya kai makura wurin kare kanninsa, ababen kaunarsa.

Shafin todaysblog9ja ne ya wallafa bidiyon wanda mutane da dama su ka dinga tsokaci iri-iri, wasu su na yaba masa yayin da wasu su ke kusarsa.

Matashin da ke shigar mata yana bara a Saudiyya ya bayyana yadda yake samun N647,000 kullum

Lamarin ya faru ne a Dammam, kusan shekaru 10 da su ka gabata inda wani dan kasar Saudiyya mai shekaru 30 da haihuwa ya kasa samun aiki bayan kammala karatuLife in Saudi Arabia ta ruwaito.

Hakan yasa watarana ya samu dabara bayan ganin yadda mabarata ke samun kudi inda ya yanke shawarar fara bara don samun kudin kashewa.

Daga nan ne yayi takardar asibiti ta bogi wacce zai nuna wa jama’a cewa yana cikin halin rashin lafiya don su tausaya masa su ba shi kudi. Sannan ya zabi wurin da jama’a ke wucewa inda ya zauna yana bara.

Da farko yana samun SR 450, wato kimanin N51,000. Daga nan mutumin ya gane cewa an fi tausayawa mata don haka ya koma yin shigar mata. A rana daya yana samun SR 5,700, wato kimanin N647,000.

Ganin yadda yake samun makudan kudaden kudaden yasa ya kara kaimi. Nan da nan dukiyarsa da ke asusun banki ta tumbatsa.

Daga nan ya yi aurensa ya ci gaba da rayuwarsa. Sannan ya bayyana yadda ya samu aiki mai kyau a Jibail Manufacturing city ya kuma siya dalleliyar mota.

Yanzu haka ya yi aure kuma Ubangiji ya azurta shi da yara biyu. Bayan wani lokaci ne ya fara shiga damuwa sakamakon zunubin da ya aikata a baya inda yake zargi dukiyar da ya samu ba halastacciya bace.

Lamarin har ya kazanta har ta kai ga yana kasa yin bacci. Sannan kuma kwatsam sai matarsa wacce bata san sana’arsa ba hakanan ta bukaci ya sake ta. Bayan ya je wurin likitan kwakwalwa ne aka gano cewa yana fama da cutar damuwa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe