28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Finafinan Hausa basa ɓata tarbiyya dama can yaranku basu da tarbiyya -Nafisa Abdullahi

LabaraiKannywoodFinafinan Hausa basa ɓata tarbiyya dama can yaranku basu da tarbiyya -Nafisa Abdullahi

Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar finafinan Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kalamai masu kaushi akan mutanen dake sukar finafinan Hausa.

Nafisa Abdullahi a wani rubutu da tayi a shafin ta na Twitter tace ko kaɗan finafinan Hausa ba sa ɓata tarbiyyar yara sai dai idan dama can asali yaran ba su samu tarbiyya a gida ba.

Akwai masu ganin cewa finafinan na gurɓata tarbiyya

Mutane da dama dai na ganin cewa finafinan Hausa na wannan zamanin na zama wani abin gurɓata tarbiyyar yara, musamman yadda ake nuna wasu abubuwan da suka ci karo da al’adar Hausawa.

An sha korafi akan yadda masana’antar ta koma nuna wasu abubuwa waɗanda suka ci karo da ɗabi’a da al’adar Hausawa, sai dai jarumar na ganin cewa masana’antar bata ɓata tarbiyya.

Nafisa Abdullahi ta caccaki masu sukar finafinan Hausa

A rubutun da jarumar tayi ta bayyana cewa ba yadda za a yi mutane su bar yaran su na kallon finanfinan ƙasar Amurka (Hollywood), finafinan Indiya (Bollywood) dana kudancin Najeriya (Nollywood), sannan su buɗe baki suce finafinan Hausa ne ke ɓata tarbiyya.

A kalamanta:

Kuna kallon finafinan Hollywood, finafinan Bollywood da finafinan turanci na Najeriya, sannan ku zo ku ce finafinan Hausa ke ɓata tarbiyya… haba? Kuna barin yaran ku su kalla, suna amfani da wayoyi da yanar gizo, amma…. finafinan Hausa ke lalata tarbiyya. Ba su da tarbiyya dama tun farko.

Mutane da dama sun yiwa jarumar martani. Ga kaɗan daga ciki:

@non-melanin ta rubuta:

Tabbas finafinan Hausa na ɓata tarbiyya fiye da sauran finafinai, dalili kuwa ke a matsayinki na Bahaushiya kin fito a matsayinki na ƴar Hausawa kai babu kallabi kin sha kaya a matse a matsayinki na ƴar musulmai, dubunnan jama’a na kallo ciki har da ƙananun yara, su kuwa can Yahudawa addinin su ya yarda musu.

@TheSuleimanAnas ya rubuta:

Wa’inchan ai’ba Hausa suke yi ba

@meerah9253 ta rubuta:

Dalla can yi mana shiru

An maka su Safara’u, Ado Gwanja, Mr 442 da sauran wasu jaruman TikTok a gaban kotu

A wani labarin na daban kuma, an maka su Ado Gwanja, Safara’u, Mr 442 a gaban wata kotun shari’ar musulunci.

An maka shahararrun mawaƙan zamani na Arewa da fitattun jaruman TikTok a gaban wata babbar kotun Shari’ar Musulunci da ke yankin Bichi na jihar Kano bisa zargin rashin ta ido wato tarbiyya.

Wasu lauyoyi ne dai suka maka mawaƙan da jaruman na TikTok a gaban kotu domin nuna adawar su bisa abubuwan da suke aikata wa

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe