32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Bana jin tsoron komai -Cewar Tukur Mamu da aka cafke a ƙasar Masar

LabaraiBana jin tsoron komai -Cewar Tukur Mamu da aka cafke a ƙasar Masar

Alhaji Tukur Mamu, fitaccen ɗan jarida mai gidan jaridar Desert Herald a jihar Kaduna, yayi magana bayan da ya shiga hannun jami’ai a ƙasar Masar.

Tukur Mamu yana daga cikin mutanen dake tattaunawa da ƴan bindigan da suka sace fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna.

An damƙe shi yana kan hanyar zuwa Umrah

A bayanan Tukur Mamu yace yana kan hanyar sa ta zuwa ƙasa mai tsarki gudanar da aikin Umrah, lokacin da aka kama shi a filin jirgin birnin Alƙhahira na ƙasar Masar inda aka tsare shi na sa’o’i 24 kuma yanzu haka za a dawo da shi gida Najeriya.

Yayin zantawa da jaridar Daily Trust akan hanyar sa ta dawowa Najeriya, Tukur Mamu yace ba a samu wani abin laifi a tattare da shi ba.

Ya kuma ƙara da cewa hukumomin ƙasar Masar sun sanar masa da cewa basu da wani dalilin da za su cigaba da tsare shi.

Ina kan hanyata ta zuwa Alƙahira-Masar amma inda na nufa Saudiyya ne domin na yi Umrah tare da wasu ƴan’uwana.

An tsare ni tsawon sa’o’i 24 a filin jirgin saman Alƙahira bisa umarnin gwamnatin Najeriya.

Ba a ci zarafi na a filin jirgin saman Najeriya ba har sai da na isa birnin Alƙahira inda jami’an tsaron wurin suka ce min hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta ba da umarnin a kama ni

An kama mu ni da iyalai na tsawon yini guda a filin jirgin saman Alƙahira. Yanzu haka sun kama jirgi na gaba domin a dawo da ni da iyalina zuwa gida Kano. Na tabbata jami’an DSS za su jira saukarmu a filin jirgin saman Kano a yau (Laraba).

Babu abinda nake boyewa sannan ba na jin tsoronsu (DSS), na rantse da Allah ba na tsoronsu, ina son kawai duniya ta san abin da ke faruwa ne. A cewar sa

A cewar sa

An sha zargin Mamu da bin tsagin ƴan ta’adda maimakon kare muradun Najeriya, zarge-zargen da yasha musantawa.

Harin Jirgin kasan Kaduna- Abuja: An kama Tukur Mamu a Misra

A wani labarin na daban kuma, an cafke Alhaji Tukur Mamu a ƙasar Masar.

Malam Tukur Mamu, mutumin da ya jagoranci ciniki tsakanin ‘yan uwan fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, da ‘yan bindiga a watan Maris ya shiga hannun ‘yan sanda a Cairo, babban birnin Misra tare da iyalansa, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda manema labarai su ka tabbatar, gwamnatin Najeriya ce ta sa a kama Mamu, wanda shi ne mai jaridar Desert Herald

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe