27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Matashin da ke shigar mata yana bara a Saudiyya ya bayyana yadda yake samun N647,000 kullum

LabaraiMatashin da ke shigar mata yana bara a Saudiyya ya bayyana yadda yake samun N647,000 kullum

Lamarin ya faru ne a Dammam, kusan shekaru 10 da su ka gabata inda wani dan kasar Saudiyya mai shekaru 30 da haihuwa ya kasa samun aiki bayan kammala karatu, Life in Saudi Arabia ta ruwaito.

Hakan yasa watarana ya samu dabara bayan ganin yadda mabarata ke samun kudi inda ya yanke shawarar fara bara don samun kudin kashewa.

Daga nan ne yayi takardar asibiti ta bogi wacce zai nuna wa jama’a cewa yana cikin halin rashin lafiya don su tausaya masa su ba shi kudi. Sannan ya zabi wurin da jama’a ke wucewa inda ya zauna yana bara.

Da farko yana samun SR 450, wato kimanin N51,000. Daga nan mutumin ya gane cewa an fi tausayawa mata don haka ya koma yin shigar mata. A rana daya yana samun SR 5,700, wato kimanin N647,000.

Ganin yadda yake samun makudan kudaden kudaden yasa ya kara kaimi. Nan da nan dukiyarsa da ke asusun banki ta tumbatsa.

Daga nan ya yi aurensa ya ci gaba da rayuwarsa. Sannan ya bayyana yadda ya samu aiki mai kyau a Jibail Manufacturing city ya kuma siya dalleliyar mota.

Yanzu haka ya yi aure kuma Ubangiji ya azurta shi da yara biyu. Bayan wani lokaci ne ya fara shiga damuwa sakamakon zunubin da ya aikata a baya inda yake zargi dukiyar da ya samu ba halastacciya bace.

Lamarin har ya kazanta har ta kai ga yana kasa yin bacci. Sannan kuma kwatsam sai matarsa wacce bata san sana’arsa ba hakanan ta bukaci ya sake ta. Bayan ya je wurin likitan kwakwalwa ne aka gano cewa yana fama da cutar damuwa.

Kuma abinda yake damunsa shi ne yadda ya tara dukiya ta hanyar bara. Yanzu haka ya zage damtse wurin shan magunguna kuma akwai alamar sauki ya fara samuwa.

An yi ram da Rabaran din da ke siyan yara musamman don azabtar da su

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas ta yi ram da wacce ake zargin tana safarar yara ne, Maureen Wechinwo, wacce ake zargin rabaran ce, kuma da kanta ta bayyana yadda take siyan yaran, Vanguard ta ruwaito.

Rundunar ta kama wasu mutane 20 da ake zargin su na safarar yara tsakanin watan Augusta da Satumba. Bayan samun bayanin sirri, an kama Maureen ne a gidanta da ke Aluu, karkashin karamar hukumar Ikwerre da ke Jihar Ribas inda aka ceto yaran guda 15.

Kwamishinan ‘yan sanda, Friday Eboka ya bayyana cewa shekarun yaran ba su wuce 7 zuwa 9 ba, inda ya kara da cewa za a yanke wa wacce ake zargin hukunci da zarar an kammala bincike.

A cewar Eboka, binciken da aka gudanar ya bayyana cewa ana dauko yaran ne daga yankin kudu-kudu, sannan a siyar mata da su.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe