29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

An maka su Safara’u, Ado Gwanja, Mr 442 da sauran wasu jaruman TikTok a gaban kotu

LabaraiKannywoodAn maka su Safara'u, Ado Gwanja, Mr 442 da sauran wasu jaruman TikTok a gaban kotu

An maka shahararrun mawaƙan zamani na Arewa da fitattun jaruman TikTok a gaban wata babbar kotun Shari’ar Musulunci da ke yankin Bichi na jihar Kano bisa zargin rashin ta ido wato tarbiyya.

Wasu lauyoyi ne dai suka maka mawaƙan da jaruman na TikTok a gaban kotu domin nuna adawar su bisa abubuwan da suke aikata wa.

Ana tuhumar su da ɓata tarbiyyar al’umma

Wasu majiyoyi sun gayawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa, ana tuhumar su da laifuffukan da suka haɗa da waƙokin rashin tarbiyya da rawar Tiktok da ke da alaƙa da lalata tarbiyyar al’umma.

Sai dai jaridar ta samu kwafin wasiƙar da kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa ƴan sanda na neman a binciki koke-koken da ke gaban masu gabatar da ƙara.

Sunayen jaruman da aka maka kotu

Wadanda aka zayyana a wasiƙar da aka aika wa kwamishinan ƴan sandan jihar Kano sun haɗa da Safara’u wacce akafi sani da Safa, 442, Dan Maraya, Amude Booth, Murja Kunya, Kawu Dan Sarki, Babiyana, Ado Gwanja, Ummi Shakira da Samha Inuwa.

Wasiƙar wacce rajistaran kotun Aminu Muhammad ya rattaɓa wa hannu na cewa:

Sakamakon ƙarar da Muhd Ali Hamza Esq, Abba Mahmud Esq, Sunusi I. Umar Esq, Abba, A.T Bebeji Esq, B.I Usman Esq, Muhd Nasir Esq, L.T Dayi Esq, G.A Badawi da Badamasi Suleiman Gandu Esq su ka gabatar.

Alƙali mai shari’a na babbar kotun Shari’ar musulunci ta Bichi a jihar Kano ya umurce ni da in rubuta tare da neman ku da ku gudanar da bincike a kan waɗanda ake zargin a sama domin ɗaukar matakin da ya dace.

An maƙala kwafin takardar korafin don ƙarin bayani. Ka huta lafiya.

Shirye-shirye sun kankama: Ado Gwanja na shirin yin wuff da Jaruma Momi Gombe

A wani labarin na daban kuma, Ado Gwanja na shirin yin wuff da jaruma Momi Gombe.

Ga dukkan alamu, lokacin auren mawaki Ado Gwanja ya matso don da kan shi ya wallafa kyawawan hotunansa a Instagram da jaruma Momi Gombe inda ya rubuta “Time”, wato lokaci.

Ita ma jarumar ta wallafa hotunansu tare inda ta ce “Alhamdulillah”. Nan da ‘yan uwan aikinsa da mutane masu musu fatan alkhairi su ka bazama su na ta kora musu addu’o’i.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe