32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Harin Jirgin kasan Kaduna- Abuja: An kama Tukur Mamu a Misra

LabaraiHarin Jirgin kasan Kaduna- Abuja: An kama Tukur Mamu a Misra

Malam Tukur Mamu, mutumin da ya jagoranci ciniki tsakanin ‘yan uwan fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, da ‘yan bindiga a watan Maris ya shiga hannun ‘yan sanda a Cairo, babban birnin Misra tare da iyalansa, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda manema labarai su ka tabbatar, gwamnatin Najeriya ce ta sa a kama Mamu, wanda shi ne mai jaridar Desert Herald. An kama shi a babban filin jirgin sama na Cairo inda ya kwashe awanni 24 a hannun jami’an tsaron kasancewar yana kan hanyarsa ta zuwa umara sannan aka maido da shi Najeriya.

Yayin tattaunawa da manema labarai, Mamu ya ce ya bar Najeriya ne a ranar Talata bayan jami’an tsaron Egypt sun gama caje shi ba tare da ganin wani abin zargi tare da shi ba.

Mamu ya bayyana cewa ya gano shirin gwamnatin Najeriya na kama shi a wata kasa kamar yadda aka yi wa mai rajin kafa kasar Yarabawa, Sunday Igboho, amma hakan ba zai yuwu a Egypt ba saboda gwamnatin kasar ta ga duk takardunsa ingantattu ne.

Idan ba a manta ba, Mamu ne ya tsaya wurin cinikin kudin fansa da ‘yan bindiga, sannan ya yi zargin gwamnatin Najeriya tana barazana da rayuwarsa.

Harin Jirgin Kasan Kaduna: ‘Yan Ta’adda Sun Sake Sako Fasinjoji 4

Halimatu Attah, tsohuwa mai shekaru 90 da aka yi garkuwa da ita a farmakin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris ta shaki iskar ‘yanci.

An sakota tare da diyarta da wasu mutum biyu kamar yadda mawallafin jaridar Desert Herald, Tukur Mamu ya bayyana, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sauran biyun da aka sako tare da tsohuwar sune Muhammad Sani Abdulmajid wanda aka fi sani da M. S Ustaz da kuma Alhaji Modin Modi Bodinga.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe