23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Najeriya za ta zama babbar mai samar da iskar gas zuwa kasashen Ketare– cewar ministan man Fetur Sylva

LabaraiNajeriya za ta zama babbar mai samar da iskar gas zuwa kasashen Ketare– cewar ministan man Fetur Sylva
Sylva9

Karamin ministan albarkatun man fetur Timipre Sylva, ya ce Najeriya na shirin zama babbar mai samar da iskar gas a Turai, sakamakon matsalar makamashin da ake fama da shi a duniya, sakamakon rikicin da ake ci gaba da yi tsakanin Rasha da Ukraine.

Mista Sylva ya bayyana haka a ranar Talata yayin wani taron koli a bikin cika shekaru 50 na Gastech Conference 2022 a Milan, Italiya.

Mai taken: “Energy Transition for Developing Nations.”

Ministan ya ci gaba da cewa, a halin yanzu, tallafin da ake samu na bunkasa iskar gas ya kasance nasara ga Turai da Afirka.

Ya ce: “A yau muna ganin ana amfani da iskar gas kuma kowace kasa za ta bukaci a kalla wasu hanyoyin samar da abinci.

“Don haka, muna so mu zama masu samar wa Turai gas. Mun riga mun fara aiki da kasar Aljeriya don gina bututun iskar gas na Trans-Sahara wanda zai dauki iskar gas din mu har zuwa Turai.
“Har ila yau, muna da haɗin gwiwa da kasar Maroko don faɗaɗa bututun iskar gas na Afirka ta Yamma zuwa Maroko da kuma tsallaken tekun Bahar Rum zuwa Turai.

“Mun yi imanin cewa Turai na buƙatar wannan iskar gas din wz da mu kuma hakan nasara ce garemu.

Mista Sylva ya bayyana a wata ganawa da ya yi da tawagar kasashen Turai a Najeriya kwanan baya, ya shawarce su da su samar da tsare-tsaren da suka dace ga bankunan su domin ba da damar zuba jari a harkar mai da iskar gas..

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe