28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Kar ku Tsoma mu cikin rikicin ku-martanin jam’iyyar APC ga PDP

LabaraiKar ku Tsoma mu cikin rikicin ku-martanin jam'iyyar APC ga PDP
Shugaban ƙasa

Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ta gargadi shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, kan jawo sunanta cikin rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.

Mista Ayu dai ya zargi jam’iyyar APC da yada labarai marasa dadi a shafukan sada zumunta domin rura wutar rikicin da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Sai dai jam’iyyar APC, a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, ta gargadi PDP da ta daina tsomata a cikin rikicinta,inda ta jaddada cewa ita bata shishigi ga me da lamurran da ke faruwa a sauran jam’iyyu.
Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ta ce: “Abin lura anan shine, shugaba Ayu yana yada maganganu don neman wanda zai yabawa laifin rikicin cikin gida da ke faruwa a jam’iyyar ta PDP.

“Irin wannan lamari na iya zama sanadiyar rugujewar jam’iyyar PDP yana gani.

“Rashin karbar alhakin magance rikicin dake afkuwa a jam’iyyar sa,, ta ya ya zai tufke wannan barakar?

“Ba kamar jam’iyyar PDP ba, APC ba ta da rade-rade kuma ba ta tsoma baki akan harkokin cikin gida na wasu jam’iyyu.

“Jam’iyyar PDP ta wuce gona da iri. Tana neman durkushewa kadan ba tare da wasu yan waje sun sa hannu ba.”

Tonon silili: Yadda Kwankwaso ya ci amana ta -Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana dalilin da yasa ya fice daga jam’iyya mai kayan marmari (NNPP) ya koma jam’iyyar PDP.

Shekarau yace Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi masa shigo-shigo ba zurfi inda yaci amanar sa da shi da magoya bayansa a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ambato cewa Shekarau ya bayyana hakan ne a yayin wata hira a gidan talabijin na Channels TV a shirin su na Siyasa a yau.

Kwankwaso ya ƙi mutunta yarjejeniyar da suka yi
Yace jagoran na Kwankwasiyga da gangan ya ƙi aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma ƙafin ya koma jam’iyyar har zuwa lokacin da INEC ta dai na amsar sunayen ƴan takara.

Mun miƙa mu su buƙatun mu, da ni da dukkanin magoya baya na da abokanan siyasa ta, sannan muka zauna da Rabiu Kwankwaso. Na miƙa masa buƙatu na kuma ya amince da su. Yace a cikin kwana ɗaya ko uku zai yi nasa daga nan zamu zauna da shi mu duba mu ga abinda zamu iya yiwa ƴan takarar daga mazaɓu daban-daban.

Ina ganin cewa ba wani babban abu bane mu zauna mu shirya ƴan takara daga ɓangaren sa da nawa. Mun yi ta jira. Na miƙa masa sunaye a ranar 10 ga watan Mayu sannan na sake tuna masa a ranar 11 ga watan Mayu. A lokacin ni da mutane na mun gama yanke shawara.

Yadda aka ci amanar Shekarau
Shekarau ya kuma ƙara da cewa yayi matuƙar mamaki da ya ga sunayen da jam’iyyar ta fitar na ƴan takara an rubuta su da hannu.

Mun gaya musu cewa sam ba zamu yarda da hakan ba, saboda a gabaɗaya cikin sunayen, suna ne kaɗai ya fito daga ɓangare na.

Abinda ya bamu mamaki, kwana biyu daganan, ɗan’uwan Rabiu Kwankwaso ya tattauna da BBC Hausa, inda yake cewa ba yadda za a yi a biya mana buƙatun mu saboda mun shiga jam’iyyar a makare. Jam’iyyar da muka shiga lokacin da ake tantance ƴan takara ana zaɓen fidda gwani?

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe