28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

An yi ram da Rabaran din da ke siyan yara musamman don azabtar da su

LabaraiAn yi ram da Rabaran din da ke siyan yara musamman don azabtar da su

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas ta yi ram da wacce ake zargin tana safarar yara ne, Maureen Wechinwo, wacce ake zargin rabaran ce, kuma da kanta ta bayyana yadda take siyan yaran, Vanguard ta ruwaito.

Rundunar ta kama wasu mutane 20 da ake zargin su na safarar yara tsakanin watan Augusta da Satumba. Bayan samun bayanin sirri, an kama Maureen ne a gidanta da ke Aluu, karkashin karamar hukumar Ikwerre da ke Jihar Ribas inda aka ceto yaran guda 15.

the totured kids
An yi ram da Rabaran din da ke siyan yara musamman don azabtar da su

Kwamishinan ‘yan sanda, Friday Eboka ya bayyana cewa shekarun yaran ba su wuce 7 zuwa 9 ba, inda ya kara da cewa za a yanke wa wacce ake zargin hukunci da zarar an kammala bincike.

A cewar Eboka, binciken da aka gudanar ya bayyana cewa ana dauko yaran ne daga yankin kudu-kudu, sannan a siyar mata da su.

Ya ce sai da su ka kwashe sa’o’i 24 kafin yaran su ka bayyana wa ‘yan sanda halin da su ka shiga, tare da cewa ana azabtar da su. Maureen Wechinwu tana da shekaru 44, kuma ana zargin Rabaran ce a wata coci.

Iyayen yaran sun bayyana irin farincikin da su ka shiga bayan an gano yaransu, inda su ka yi bayani dalla-dalla dangane da ranar da aka sace yaran da kuma halin da su ka shiga.

A tattaunawar da aka yi Maureen ya kada baki ta ce:

“Ina aiki ne da gidan marayu inda ake kawo ‘ya’yan mahaukata. Fransisca Onyinyechi, wacce wata mahaukaciya ta haifa a kasuwar Ogbogoro tana daya daga cikin yaran.

“Ba zan kira kaina da rabaran ba, saboda na tafa abin kunya. Amma na yarda a baya ni rabaran ce. Kuma wani lokacin wani Victor ya na kawo min yara inda yake bukatar kudi a hannuna. Wani lokacin ina ba shi N50,000, N60,000 ko N100,000.”

Yadda jama’an gari su ka fatattaki uba da diyarsa bayan ya lalata ta har ta haifi yara 2

Jama’an sun kori wani mutum daga garinsu bayan ganin ya koma zaman lalata da diyarsa ta cikinsa bayan an tambayeta kuma ta bayyana gaskiya, LIB ta ruwaito.

Dama tun farko an kori Amaechi Agnalasi da diyarsa, Queen Bassey daga garin Nnobi da ke jihar Anambra bayan gano su na lalata da juna har sun haifi yara biyu.

Ta bayyana yadda mahaifinta ya dinga lalata da ita kuma ya sanya ta tayi alkawarin ba za ta sake kula wani ba sai shi.

Yayin da ake titsiye shi don ayi masa tambayoyi, Amaechi ya ce ya tilasta diyarsa ta yi masa rantsuwa saboda ba ya so ta bar shi.

Ya ce sauran yaransa sun tsere, hakan yasa ya yi hakan don kada Queen ta bar sa ya fara lalata ta ta.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe