27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wata budurwa mai rawar TikTok a masallaci ta faɗa komar ƴan sanda

LabaraiWata budurwa mai rawar TikTok a masallaci ta faɗa komar ƴan sanda

Ƴan sanda a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan sun cafke wata budurwa mai amfani da manhajar TikTok bisa laifin tiƙar rawa a masallaci.

An kama budurwar ne tare da ƴan tawagarta a ranar Litinin bayan bidiyonta tana rawa a masallacin Faisal ya ƙaraɗe shafukan sada zumunta. Jaridar Islamic Information ta rahoto.

Limamin masallacin ya kai ƙorafi akan budurwar

Limamin masallacin Mohsin Ishaq shine ya shigar da ƙorafi akan budurwar da ƴan tawagarta a ciki har da mai ɗaukar bidiyon, a ofishin ƴan sanda na Margalla bisa tanadin dokar PPC 295-A.

A cikin ƙorafin na sa ya bayyana cewa yaga wani bidiyo a shafukan sada zumunta na wata budurwa ba sanye da kallabi ba kuma cikin shiga mara kamala. Kwatsam kawai sai ta shiga cikin harabar masallacin na Faisal inda ta keta rigar mutuncin wurin ibadar.

Matasa sun rungumi ɗabi’ar rashin kamala a shafukan sada zumunta

A cewar ƙorafin da aka shigar, tunda limamin masallacin musulmi ne kuma ɗan ƙasar Musulunci ta Pakistan, hakan ya taɓa ƙimar addinin sa, inda ya ƙara da cewa irin wannan rashin mutunta addini ya fara zama ruwan dare a shafukan sada zumunta a tsakanin matasa.

A cewar takardar ƙorafin da aka shigar, akwai nauyi akan mu na ganin mun daƙile aukuwar irin waɗannan abubuwan.

Ana shigar da ƙorafin, ƴan sanda suka bazama bincike tare da tuntuɓar sauran hukumomi inda aka gano budurwar tare da sauran waɗanda ake zargin.

Kotu ta yankewa tsohon limamin masallacin Harami shekara 10 a gidan kaso

A wani labarin na daban kuma, kotu ta yankewa tsohon limamin masallacin Harami shekara 10 a gidan yari.

Wata kotu a ƙasar Saudiyya ta yanke wa tsohon limamin masallacin Harami, Sheikh Saleh al Talib, hukuncin shekara goma a gidan kaso.

A cewar wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta ƙasar Amurka mai suna Democracy for the Arab World Now (Dawn), kotun ɗaukaka ƙarar laifuka ta musamman a birnin Riyadh ta tura Sheikh  Saleh al Talib zuwa gidan kaso bayan ta soke wankewar da akayi masa da farko

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe