23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Saurayi ya yashe komatsan budurwarsa kaf ya yi sadaka da su bayan kama ta tana cin amanarsa

LabaraiSaurayi ya yashe komatsan budurwarsa kaf ya yi sadaka da su bayan kama ta tana cin amanarsa

Wani saurayi ya yashe kaff komatsan budurwarsa inda ya yi sadaka da su bayan kama ta da wani saurayin tana cin amanarsa, LIB ta ruwaito.

Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, wanda makwabcinsu ne ya bayyana yadda yanzu haka budurwar ta bi kawayenta inda su ka yi tafiya.

A cewarsa, cikin fushi da neman daukar fansa yasa saurayin ya dauki wannan matakin don yanzu haka da wuya idan budurwar ta san halin da ake ciki.

Ya wallafa hotunan komatsan budurwar yayin da saurayin ke yin sadaka da su.

A cewar mai labarin mai suna camhoudini:

Makwabcina ya kama budurwarsa taba cin amanarsa, bai ce mata komai ba, sai da ya bari ta yi tafi tare da kawayenta sai ya kyautar da kayanta a matsayin sadaka. Ranar Juma’a zai sauya gida ya koma wani na daban. Ita kuma ranar Talata mai zuwa za ta dawo, bata san inda zai koma ba.

Ni nake taya shi kwashe kayan. Sannan ya ci gaba da tura mata sako tamkar babu abinda ke faruwa. Yana da shirin sauya lambar waya da zarar ya ji za ta hau jirgi don ta dawo gida.”

Yadda wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta kan yunkurin yiwa ƴar ta fƴaɗe

Wata mata mai shekara 36 a duniya, ta yanke mazakutar saurayin ta mai shekara 32 a duniya, da wuƙa bisa zargin ƙoƙarin yiwa ɗiyarta mai shekara 14 a duniya fyaɗe.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa lamarin ya auku ne a yankin Lakhimpur Kheri, a jihar Uttar Pradesh ta ƙasar Indiya.

Tare matar da saurayin suke rayuwa

A cewar jami’ai, matar da ƴar ta suna rayuwa tare da mutumin na tsawon shekara 2 bayan ta rabu da tsohon mijinta mai shan giya.

Matar wacce ta shaidawa Times of India cewa tana aiki ne a gona lokacin da lamarin ya auku.

Tayi iƙirarin cewa ta isa gida akan lokaci inda ta kama saurayin nata dumu-dumu yana ƙokarin yin fƴaɗe ga ɗiyar ta.
Matar ta kuma ce ita ma yayi ƙoƙarin kai mata hari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe