28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Har kin manta lokacin da Ghana-mas-gonki ki ka zo birni, inji Tsohon saurayin Fati Washa

LabaraiKannywoodHar kin manta lokacin da Ghana-mas-gonki ki ka zo birni, inji Tsohon saurayin Fati Washa

Wani bidiyon da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani an ga wani matashi yana wakar habaici bayan wallafa hotonsa tare da kyakkyawar jarumar Kannywood mai tashe, Fati Washa.

A bidiyon da Labaran Hausa ta dauko daga shafin Kannywood Empire na Instagram, an ga matashin tsaye yana rera wakar yayin da ya makala hotonsa da jarumar.

Da alamu hoton da su ka dauka tare a lokacin ba ta waye ba don wani kallabi ta daura har goshinta, yayin da ya ke tsaye kusa da ita sanye da bakin gilashi.

Sai kuma ya makala hotonta na yanzu sanye da suttura masu kyau da kuma aji.

Anan ne yake yin baitukan waka kamar haka:

“Har kin manta lokacin da da Ghana-mas-gonki kinka zo birni, wai yanzu kin kile babu abokin fadanki sai ni.

“Karshen munafiki jin kunya, je ki ba ruwana ni. Za ki yi danasani Amma ni dai ban miki fata ba.”

Ga bidiyon:

Nan da nan jama’a su ka nufi karkashin bidiyon su na ta yi masa tsokaci.

Classy__variety yace:

Babu wani danasanin da zata yi.”

Zulfat_algudan tace:

Dan bakin ciki ne Wallahi.”

Salxahh tace:

“Wakar ta yi dadi.”

Zainabsunusi293 ta ce:

“Kai, tonon silili.”

Kwaise47 tace:

“To sunnu, yanzu dai ta yi maka nisa.”

Daga direba zuwa mai mota: Saurayi ya nuna cigaban da ya samu bayan budurwar sa ta kyale shi don yana tuƙi

Bidiyon wani saurayi wanda ya nuna cigaban da ya samu a rayuwa tun bayan da budurwar sa ta rabu da shi, ya ɗauki hankulan mutane a yanar gizo.

Saurayin ya nuna cigaban da ya samu

A yayin shiga wata gasa a manjahar TikTok, saurayin ya nuna tsofaffin hotunan sa yana jikin wata babbar mota inda ya bayyana cewa budurwar sa ta rabu da shi saboda yana tuƙin babbar mota. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

A cikin wata sabuwar ɗauka kuma a cikin bidiyon da ya wallafa, saurayin ya shiga cikin wani ɗaki sanye da tufafi mai kyau mai ɗaukar hankali.

Saurayin mai suna Tom Shahonya, ya bayyana cewa yanzu shi yana da babbar mota mallakin kan sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe