24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Na ritsa mijina da mahaifiyata turmi da tabarya, wanne mataki ku ka ga ya dace in dauka?, Matar aure

LabaraiNa ritsa mijina da mahaifiyata turmi da tabarya, wanne mataki ku ka ga ya dace in dauka?, Matar aure

Wata matar aure da ke zama a Jihar Gombe amma mijinta yana aiki a Abuja ta bayyana yadda da tsakar dare ta ritsa mijinta da mahaifiyarta su na lalata, kuma har ta gansu ta bar wurin ba su kula da ita ba, shafin Suhaima M Fulani na Facebook ya ruwaito.

A cewarta, tun da take zaune da mijinta, bai taba bata mata rai ba ko kuma yayi mata wani abu na musgunawa, amma a wannan karon kanta ya kulle sakamakon abinda ta gane wa idanunta.

Ta fara da bayyana yadda mahaifinta ya rasu, hakan yasa bata da wacce ta wuce mata mahaifiyarta. Bayan ta haihu ne mahaifiyarta ta je gidanta da ke Gombe don tayi makonni uku na zaman jego.

Sai dai a cewarta, dama kullum sai mijinta ya bata Fura, ashe yana sanya mata maganin bacci a ciki, amma ranar da dubunsu za ta cika bata sha furar bane.

Ta bayyana yadda falkawarta ke da wuya, sai bata ga mijinta a gefenta ba, hakan yasa ta yi tunanin ko ya shiga ban daki ne, kasancewar dakuna biyu na kwana gare su, sai ta yanke shawarar komawa dayan dakin don ta yi amfani da bayin.

Shigarta ke da wuya ta ga mijinta da mahaifiyarta su na lalata, sai Ubangiji ya sanya mata nutsuwa ta lallaba ta koma daki ta kwanta cike da damuwa.

Hakan yasa take neman shawarar yadda za ta bullo wa lamarin.

Yadda wata matar aure ta kama ƙanwarta na lalata da mijinta akan gadon auren su

Wata budurwa a shafin Twitter ta bayyana cewa ta gano mata suna da saurin yafewa mazajen su idan suka kama su suna keta haddin igiyar aure. Ta faɗi hakan ne bayan wata matar aure ta yafewa mijinta amma ta ƙori ƙanwarta bayan ta kama su suna lalata tare.

Budurwar wacce ke amfani da sunan @Ada_nnempi a Twitter, ta bayyana wannan binciken na ta ne a shafin inda ta bayyana abinda wata matar aure tayi bayan ta kama ƙanwarta da mijinta suna saduwa tare.

Matar auren ta sha alwashin rabuwa da ƙanwarta

Tace matar auren da mijinta ya kwanta da ƙanwarta, ta sha alwashin ta raba gari da ƙanwarta ta har abada.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa Ada_nnempi tace matar auren da abin ya faru da ita, itace ta gaya mata yadda mummunan lamarin ya auku. Ta ce ta tausaya mata da ita da ƙanwarta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe