24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Labari mai daɗi: Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ƙara haraji kan ɓangaren sadarwa

LabaraiLabari mai daɗi: Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ƙara haraji kan ɓangaren sadarwa

Gwamnatin tarayya a Najeriya ta dakatar da shirinta na ƙara yawan harajin da take amsa daga kiran waya, Data da sauran ayyukan sadarwa.

Jaridar Vanguard ta ambato ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana haka a ranar Litinin, a wurin wani taron ƙaddamar da kwamitin shugaban ƙasa kan harajin aiki na ɓangaren tattalin arziƙin zamani a birnin Abuja.

Ɓangaren sadarwa na fama da yaean haraji kala-kala

Sheikh Pantami yace ɓangaren sadarwa yana fama da yawan haraji kala daban-daban waɗanda suka wuce ƙima.

Sheikh Pantami ya kuma ƙara da cewa a karan kansa baya goyon bayan ƙara yawan harajin, wanda ko tantama babu zai ƙara tsadar kuɗin kiran wayar salula, da mutane ke kashewa.

Tun a baya dai gwamnatin tarayyar ta hannun ofishin kasafin kuɗi na ƙasa ta bayyana cewa zata fara aiki da sabon harajin aikin kan harkokin sadarwa da kayan maƙulashe a shekarar 2023.

Gwamnatin tarayya zata kara kashi 5% na haraji kan kiran wayan salula

A wani labarin da jaridar labarunhausa ta kawo muku kuma, gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin ƙara kashi 5 na haraji kan kiran wayar salula.

Nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara biyan harajin kashi 12.5 na ayyukan sadarwa a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke shirin kara harajin kaso biyar wanda ya hada da ayyukan sadarwa a Najeriya.

Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da haraji kan ayyukan sadarwa a Najeriya ranar Alhamis a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, za a kara biyar akan kashi 7.5 na haraji da ake biya a da wato VAT, kan ayyukan sadarwa.

Misis Ahmed, wacce ta samu wakilcin mataimakin babban jami’in ma’aikatar, Frank Oshanipin, ya ce karin harajin kashi 5 dama yana cikin dokar kudi tun shekarar 2020 amma ba a aiwatar da shi ba.

Ta ce an samu tsaikon aiwatar da shi ne sakamakon cudanya da gwamnati da masu ruwa da tsaki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe