28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen gina sabon birni wanda zai yi gogayya da Dubai

LabaraiGwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen gina sabon birni wanda zai yi gogayya da Dubai

Gwamnatin Tarayya da manhajar cryptocurrency Binance Holdings Ltd sun fara tattaunawa dangane da yadda za su gina wani katafaren wuri na bunkasa tattalin arziki musamman don taimaka wa masu sana’o’i don su inganta su da fasahar zamani, Legit.ng ta ruwaito.

Kamar yadda Hukumar Nigerian Processing Zone ta bayyana a wata takarda, hadin guiwar ta su zai samar da wata cibiya ne mai kama da ta kasar Dubai.

Bloombergs ta ruwaito cewa gwamnatin Tarayya ta na so ta yi amfani da cibiyar wurin raba kafa dangane da hanyar samun kudin shiga baya ga man fetur, hakan zai bayar da dama wurin karo hanyoyin hada-hadar kasuwanci da kuma shige da fice a kasar.

Harkar Cryptocurrency ta samu karbuwa sosai musamman ga matasan Najeriya tsawon shekaru, idan aka gina wannan za a samu ci gaba da kuma bunkasar darajar Naira maimakon yadda kullum take sauka a kasuwannin canji.

Yayin da CoinGecko, wani mai nazari dagane da cryptocurrency yayi bincike, ya gano cewa ‘yan Najeriya sun fi ‘yan ko wacce kasa fara tara cryptocurrency tun bayan harkar ta fara yin kasa a watan Afrilu.

Sannan wadanda su ka fara harkar Interswitch Ltd da Flutterwave Inc. sun tara dukiya mai kimar biliyoyi yanzu haka.

Gwamnatin tarayya zata kara kashi 5% na haraji kan kiran wayan salula

Nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara biyan harajin kashi 12.5 na ayyukan sadarwa a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke shirin kara harajin kaso biyar wanda ya hada da ayyukan sadarwa a Najeriya.

Hukumar sadarwa ta shirya taro

Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da haraji kan ayyukan sadarwa a Najeriya ranar Alhamis a Abuja.
Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ce ta shirya taron.

Za a kara kashi 5% akan wanda ake biya a da

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, za a kara biyar akan kashi 7.5 na haraji da ake biya a da wato VAT, kan ayyukan sadarwa.

Wannan kari ne da aka dade da aiwatarwa

Misis Ahmed, wacce ta samu wakilcin mataimakin babban jami’in ma’aikatar, Frank Oshanipin, ya ce karin harajin kashi 5 dama yana cikin dokar kudi tun shekarar 2020 amma ba a aiwatar da shi ba.
Ta ce an samu tsaikon aiwatar da shi ne sakamakon cudanya da gwamnati da masu ruwa da tsaki.
Za a biya ne a kowane wata, a ranar 21 ko kafin nan wanda biyan zai zama ko kowane wata.
“Ba a kayyade adadin harajin a cikin dokar ba, domin hakkin shugaban kasa ne ya daidaita kudin harajin kuma ya kayyade kashi biyar bisa dari na ayyukan sadarwar da suka hada da GSM.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe