24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

‘Yan bindiga sun yi barazanar kashe jami’in Dan sanda reshen Birnin Gwari na jihar Kaduna Sani Mohammed wanda aka yi garkuwa da shi a watan Yuni a lokacin da yake bakin aiki.

Labarai'Yan bindiga sun yi barazanar kashe jami’in Dan sanda reshen Birnin Gwari na jihar Kaduna Sani Mohammed wanda aka yi garkuwa da shi a watan Yuni a lokacin da...
WhatsApp Image 2022 09 04 at 10.49.01 e1662296136446 779x570.jpeg

An yi garkuwa da Mista Muhammad, babban Sufeton ‘yan sanda ne tare da matafiya da dama a kan babbar hanyar Birnin Gwari da ke fama da matsalar tsaro yayin da yake ba da rahoto a matsayin sabon DPO na yankin.

An yi masa chanjin aiki ne daga Panbegua dake karamar hukumar Kubau, zuwa Birnin Gwari.
An yi garkuwa da shi ne bayan da ‘yan bindigar suka mamaye ayarin motocinsa.

A ranar Lahadin da ta gabata, kanin jami’in da aka yi garkuwa da shi, Adamu Abdullahi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun sayar da duk wani abu da suke da shi domin biyan kudin fansa amma har yanzu ‘yan bindigar na neman a kara musu tare da yin barazanar kashe shi.

“Jami’in ya shafe kwanaki 69 a tsare, ‘yan uwa mun yi abin da za mu iya, mun biya Naira miliyan 7 kudin fansa domin a sako shi amma har yanzu ‘yan bindigar suna tsare da shi, suna neman a biya su Naira miliyan 20,” Cewar Abdullahi

Mista Abdullahi ya ce ‘yan bindigar sun ba su zuwa ranar Laraba mai zuwa domin su kammala biyan kudin fansa idan ba haka ba, za su kashe shi.

Ya ce sun ziyarci rundunar ‘yan sandan Kaduna sau uku domin matsa lamba don a ceto shi amma har yanzu kokarinsu bai kai ga ceto abokin aikin nasu ba.
Muna rokon Shugaba Muhammadu Buhari, Sufeto Janar na ‘yan sanda, da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, da su taimaka a ceto shi.

“Ana azabtar da matarsa da ‘ya’yansa, dole ta sa mu ka kwace wayoyinsu domin duk lokacin da ‘yan bindigar suka kirasu suna yi musu barazanar kashe shi, wanda hakan kansa matarsta ta suma.

“’Yan uwanmu ciki har da mahaifin mu mai shekara 90 muna cikin mawuyacin hali. Sun ba mu wa’adin karshe na kawo kudin fansa ko kuma kafin ranar Laraba su hallaka shi,” in ji Mista Abdullahi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce babu wani jami’insu da zai fada hannun masu garkuwa da mutane su yi watsi da shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalige, ya shaida wa wailing Premium Times cewa, ana kokarin kubutar da dan sandan.

Mista Jalige ya ce matakin da rundunar ta dauka ba lallai ba ne jama’a su san halin da ake ciki har da dangin jami’in da aka sace.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe