29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ƙasar Qatar ta amince a siyar da giya kafin fara wasanni a gasar cin kofin duniya

LabaraiƘasar Qatar ta amince a siyar da giya kafin fara wasanni a gasar cin kofin duniya

Ƙasar Qatar zata ba ƴan kallo damar siyan giya a yayin wasannin cin gasar kofin duniya wanda zaa gudanar wannan shekarar a ƙasar

Iznin siyan giyar zai fara ne sa’o’i uku kafin a fara wasa da kuma sa’a ɗaya bayan kammala wasa. Sai dai ba zaa siyar da giya ba a lokutan da ake buga wasa. Kamar yadda wata majiya ta sanarwa jaridar CNN.

Kamfanin Budweiser ne zai siyar da giya a gasar kofin duniya

Kamfanin giya na Budweiser, wanda yake ɗaukar nauyin gasar kofin duniya, shine aka sahalewa siyar da giya a yayin gasar. Kamfanin zai siyar da giyar ne a wurin da ake bayar da tikiti ba a wurin da ƴan kallo ke zama ba a filayen wasa, a cewar majiyar.

Gasar cin kofin duniya ta wannan shekarar itace ta farko da zaa gudanar a ƙasar musulmai wacce take da tsauraran dokoki akan shan giya. Hakan ya zama ƙalubale ga masu shirya gasar wacce kamfanin giya ke ɗaukar nauyin ta wacce akasarin ƴan kallo ke shan giya.

Lokutan da zaa riƙa siyar da giya

Zaa samar da giya lokacin da aka buɗe ƙofofin filayen wasa wanda yayi daidai da sa’o’i uku kafin a fara wasa. Duk mai son sha zai iya sha a lokacin. Sannan bayan sun bar filayen wasa da kuma sa’a ɗaya bayan an tashi daga wasa. A cewar majiyar

Haka kuma kamfanin na Budweiser zai siyar da giya a dandalin masu kallo a tsakiyar birnin Doha daga ƙarfe 6:30 na yamma zuwa 1:00 na dare, a kowace rana cikin ranaku 29 na gasar, wacce zaa fara a 20 ga watan Nuwamba, 2022.

Saudiyya: Kotu ta yankewa tsohon limamin masallacin Harami shekara 10 a gidan kaso

A wani labari na daban kuma, kotu ta yankewa tsohon limamin masallacin Harami shekara 10 a gidan kaso.

Wata kotu a ƙasar Saudiyya ta yanke wa tsohon limamin masallacin Harami, Sheikh Saleh al Talib, hukuncin shekara goma a gidan kaso.

A cewar wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta ƙasar Amurka mai suna Democracy for the Arab World Now (Dawn), kotun ɗaukaka ƙarar laifuka ta musamman a birnin Riyadh ta tura Sheikh  Saleh al Talib zuwa gidan kaso bayan ta soke wankewar da akayi masa da farko

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe