24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

‘Yan ta’adda sun kai hari masallaci, sun yi awon gaba da wasu mutane a jihar Zamfara

Ilimi'Yan ta'adda sun kai hari masallaci, sun yi awon gaba da wasu mutane a jihar Zamfara
Armed Bandits 1140x570 1

Wasu ‘yan ta’adda a kan babura sun kai hari wani masallacin Juma’a a ranar Juma’a tare da yin garkuwa da wasu masu ibada a unguwar Zugu da ke yankin Bukkuyum a jihar Zamfara.

Majiyoyi da dama na cikin gida sun shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa ‘yan ta’addan ba su yi navarre Katherine kowa ba a garin a inda harin ya dauki sama da sa’a guda.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da sace mutanen amma ta ce ba za ta iya tabbatar da adadin wadanda aka sace ba.

Harin ya faru ne jim kadan kafin zuwan babban Limamin da zai jagoranci Sallah, an harbe wani mutum guda mai suna Habibu Fada, kuma an kai shi asibiti.

“An harbe shi ne a lokacin da yake kokarin guduwa a lokacin da ‘yan bindigar suka far wa masallacin. Bai sani ba sun zagaya masallacin. Suna tsani idan suka umurci mutane su taru wuri daya wani ya nemi ya gudu,” dan’uwansa, Sheriff Fada ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Ya kara da cewa an garzaya da shi wani asibiti da ke Gummi, bayan ‘yan bindigar sun tafi.

Mista Fada ya ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu mazauna yankin da suka hada da abokansa da ‘yan uwansa.

Wani mazaunin garin Yasir Sahabi ya ce harin bai rutsa da shi ba sakamakon zuwa masallaci a makare.
‘Yan bindiga sun kama abokinsa Usman Junaidu. Ya je masallaci da wuri kuma ni ma ya kamata ace tare da shi muka tafi amma ban ma san dalilin da ya sa ban je da wuri ba kamar yadda muka saba. Na yi always na kama hanya, sai na ji karar harbe-harbe, sai ga mutanen da ba su isa masallaci ba, suna gudu. A lokacin ne ni ma na fara gudu,” in ji Mista Sahabi.

Ya ce mataimakin babban Limamin da ya gudanar da hudubar khuduba da Kiran sallah yana daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Ko da yake kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda aka sace ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, wani mazaunin garin, Bashiru Dantanin, ya ce tun bayan harin mutane 44 ba a gan su ba.

Duk da cewa wasu mazauna yankin sun tsere daji saboda tsoron kada a sace su, Mista Dantanin ya ce har yanzu al’umma na ci gaba da tattara sunayen wadanda suka bata.

“Ya zuwa yanzu, mun kirga mutane 44 da ba a gani ba.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar da harin amma ya ce har yanzu ba a tantance adadin wadanda aka sace ko kuma inda aka kai su ba.

“Mun samu rahoton harin kuma mun tabbatar da cewa an sace wasu mazauna garin. Har yanzu ba a tantance adadin wadanda aka kama ba kuma ba mu san ko suna cikin masallaci ko wani wuri a yankin ba amma abu mafi mahimmanci shi ne an kai hari,” inji shi.

Ya ce rundunar ta dauki matakin ceto wadanda aka sace.

Yan sanda sun chafke matar da ta hada baki aka yi garkuwa da mijinta

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a ta gurfanar da wata mata mai suna Joy Emmanuel ‘yar shekara 40 bisa zargin shirya garkuwa da mijinta, Emmanuel Ebong.

Kwamishinan ‘yan sanda, Olatoye Durosinmi, ya shaida wa manema labarai cewa, Joy da sauran masu garkuwan sun karbi kudi naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa domin a sako mijinta.

Mista Durosinmi ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen zakulo masu aikata irin wadannan laifuka.
Da take zantawa da manema labarai, Joy ta ce matsin rayuwa ne ya tilasta mata shirya yin garkuwa da Ebong.
Ta ce mijinta bayan kashe ta da kin kwanciyar aure har da sauran hakkoki baya iya saukewa.

“Na kan yi wasu ‘yan kananan ayyuka don ciyar da iyalina. Na shirya sace shi ne saboda ina bukatar kuɗi don in kula da iyalina.
“Abin takaici, bayan anyi nasarar samun kudin fansar ban samu ko sisi ba,” in ji ta.

Misi Joy ta ambaci wani Udo Moji, a matsayin shugaban kungiyar da suka sace mijinta.

Ta ce: “Sun karbo min kudin sai dai basu bani komai ba. Wasu daga cikin ‘yan kungiyar da aka kama suna kashe kudi sune suka ambaci sunana ga ‘yan sanda.”
Shi ma da yake magana, Mista Ebong ya ce an yi garkuwa da shi ne da misalin karfe 8.30 na dare, a ranar 21 ga watan Yuli jim kadan bayan shigarsa gidansa.

“Sun dauko ni a gida a cikin wata karamar bas. Sun tsare ni har na tsawon kwanaki hudu in da suka nemi kudin fansa Naira miliyan biyu.

“Sun kai ni Etinan inda suka tsare ni. Cikin sa’a sai ga ‘yansanda.

‘Naira Miliyan biyu suka karba. ‘yan sanda sunyi nasarar kwato N500,000 daga hannunsu,” inji shi.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe