27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wata baturiya ta musulunta bayan karanta Al-Qur’ani

IlimiWata baturiya ta musulunta bayan karanta Al-Qur'ani

Bayan ta karanta Al-Qur’ani mai girma sau huɗu a wata ɗaya, wata mata mai suna Maryum  a birnin Plymouth wacce ta taso cikin addinin kirista ta musulunta. 

Wannan matakin da ta ɗauka na musulunta ya ƙada hantar ƴan’uwanta da abokai, inda har kakar ta ke bayyana musuluntar ta a matsayin ta wani ɗan lokaci ce. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Mata na musulunta a Plymouth

Duk da cewa ba musulmai sosai a Plymouth, mata uku ne suka musulunta a lokacin azumin watan Ramadan da ya gabata.

Maryum ta taso a gidan mabiya addinin kirista sannan tayi imani da Allah. Bayan ta fara girma ta wuce shekara goma a duniya, sai ta fara ja da baya, ta kasa fahimtar alfanun zuwan coci ranar Lahadi, amma dai ta cigaba da tafiya a hakan saboda abinda aka koya mata kenan.

Yadda ta shigo addinin musulunci

Tafiyarta ta shigowa musulunci ta fara ne bayan ta fara karantar wasu abubuwa a cikin sauran addinai a jami’a. Sai dai, hirar da tayi da wani mai gyaran wuta ne wanda yazo yi mata gyara a gida bayan an tashin bam ɗin birnin Manchester ya sanya taji ƙarin ƙarfin guiwar yin bincike sosai akan addinin musulunci.

Ina duba wayata sai nayi sharhi da cewa ‘wannan yayi muni da yawa’ sai yace min ‘kina tunanin musulman ƙwarai haka suke? Sai na ce masa ban san wani musulmi ba.

Hakan ya sanya Maryum yin bincike akan addinin musulunci. A watan azumin Ramadan da ya gabata, Maryum ta karanta Al-Qur’ani sau huɗu cikin fassara, da kuma ƙara yin bincike kan wuraren da bata fahimta ba

Da farko niyya ta kawai sanin abinda Al-Qur’ani yake koyarwa. Akwai mutanen da ke ɗaukar wani ɓangare na Al-Qur’ani suna mai fassarar yana koyar da rikici da tsana.

Wata mata mai tsananin kyamar addinin Musulunci ta musulunta 

A wani labarin na daban kuma, wata mata mai tsananin ƙyamar addinin musulunci ta musulunta.

Wata likitar yara ‘yar asalin kasar Netherlands mai suna  Paulin, ta karbi addinin musulunci. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe