24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Bidiyo: Yadda Bishop Kukah ya kwashi rawar wakar ‘Buga’ a bikin cikarsa shekaru 70

LabaraiBidiyo: Yadda Bishop Kukah ya kwashi rawar wakar 'Buga' a bikin cikarsa shekaru 70

A wani sabon bidiyo wanda ya ke ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an ga fitaccen bishop din na addinin kirista, Matthew Kukah yana kwasar rawar fitacciyar wakar nan ta Kiss Daniel, Buga, Qed TV ta ruwaito.

Wannan lamari ya dauki hankalin mutane da dama masu amfani da kafafen sada zumunta musamman. Saboda rawa ne na matasa.

Bishop Kukah fitaccen fasto ne na addinin kirista a shiyyar Sokoto. Kuma ya dade ya na samun matsaloli daban-daban da musulmai a yankin.

Dama tun bayan bullar wakar Buga ta yi matukar farinjini wanda hakan yasa a gidajen biki, suna da sauran wuraren taro ake yawan sa ta saboda jama’a su na sonta.

A wannan karon kuwa a bikin cikar Bishop din shekaru 70 aka gansa yana kwasar rawar wakar cike da nishadi.

Cikin abokansa da su ka isa wurin taya shi murnar har da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi da sauran manyan mutane.

Sun kwashi nishadi kwarai wanda mutane kuma su ka dinga mamakin inda ya koyi wannan rawa ta zamani kasancewarsa malamin addini.

Ga bidiyon a kasa ku sha kallo:

Bidiyon wata Amarya tana kwasar rawa a liyafar aurensu yayin da ango ya zauna takaici ya ishe shi

A wani guntun bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani an ga inda amarya ta zage a liyafar aurenta tare da kawayenta tana kwasar rawa yayin da angonta ya shiga damuwa, Shafin Arewa Fashion Style ne ya ruwaito.

Tun a bidiyon idan mutum ya kula zai ga yadda angon ya koma kan kujera ya zauna yayi tagumi da alamu duk abin duniya ne ya ishe shi.

Ita kuma amaryar ta ci gaba da rawarta inda ta nuna halin ko in kula tare da kwayenta.

Mutane da dama sun yi tsokaci yayin da suke cewa ta yiwu angon yana jin haushin rawar tata ne ko kuma dai bai san zata iya wannan rawar haka ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe