23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda jama’an gari su ka fatattaki uba da diyarsa bayan ya lalata ta har ta haifi yara 2

LabaraiYadda jama'an gari su ka fatattaki uba da diyarsa bayan ya lalata ta har ta haifi yara 2

Jama’an sun kori wani mutum daga garinsu bayan ganin ya koma zaman lalata da diyarsa ta cikinsa bayan an tambayeta kuma ta bayyana gaskiya, LIB ta ruwaito.

Dama tun farko an kori Amaechi Agnalasi da diyarsa, Queen Bassey daga garin Nnobi da ke jihar Anambra bayan gano su na lalata da juna har sun haifi yara biyu.

Ta bayyana yadda mahaifinta ya dinga lalata da ita kuma ya sanya ta tayi alkawarin ba za ta sake kula wani ba sai shi.

Yayin da ake titsiye shi don ayi masa tambayoyi, Amaechi ya ce ya tilasta diyarsa ta yi masa rantsuwa saboda ba ya so ta bar shi.

Ya ce sauran yaransa sun tsere, hakan yasa ya yi hakan don kada Queen ta bar sa ya fara lalata ta ta.

Ga bidiyon mutumin yayin yake fadin hujjarsa ta yin hakan:

Kotu ta daure wani matashi bayan karuwa ta mutu su na tsaka da lalata

Wata kotun majistare da ke Akure a Jihar Ondo ta umarci a daure wani Dele Ebenezer, mai shekaru 31 bisa zarginsa da zama sanadiyyar mutuwar wata karuwa, LIB ta ruwaito.

Dan sanda mai gabatar da kara, Omhenimhen Augustine ya sanar da kotu cewa ana zarginsa da halaka Blessing Eze mai shekaru 47, sanadiyyar lalatar da yayi da ita.

Augustine ta bayyana yadda mamaciyar ta shiga mawuyacin yanayi yayin da su ke tsaka da lalatar wacce ta yi sanadin mutuwarta.

Ana zarginsa da aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Yunin 2022, da misalin karfe 4 na safiya a Otal din Cool Corner cikin Ondo, sai dai bai amsa laifin ba.

A cewarsa Augustine, laifin ya ci karo da sashi na 316(2) kuma hukuncinsa na karkashin sashi na 319 na dokar Criminal Code Cap 37. Volume 1, na dokokin Jihar Ondo, 2006.

Lauyan wanda ake zargi, C. O Falana ya bukaci kotu ta ba shi damar yin rantsuwa.

Alkalin kotun, O. R Yakubu ya bukaci a sakaya wanda ake zargin a magarkamar ‘yan sanda sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Yulin 2022.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe