29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wani matashi ya hallaka dan uwan sa har lahira saboda rashin biyan kudin wutar lantarki

LabaraiLabaran DuniyaWani matashi ya hallaka dan uwan sa har lahira saboda rashin biyan kudin wutar lantarki
Fyaɗe

Wani matashi ya harbe yayan sa bisa rashin biyan kudin wutar lantarki a Uruagu, karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra, kudu maso gabashin Najeriya.

Ya zargi dan uwan sa da yanke masa wuta

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin, Peter Orji, ya zargi babban yayansa, Godwin Orji, da dage masa wutar lantarkin sa.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata.

Ya kasa biyan kudin wutan gidan sa

An dai ce wanda ake zargin ya kasa biyan kudin wutan bangaren sa har Naira 1,500 duk wata, wanda hakan ya sa wanda hakan ya tunzura wanda aka kashe ya yanke wutan gidan kanin nasa.

Wanda ake zargin ya fusata wanda hakan yasa ya tunkari dan uwan sa.

Rkici ya barke tsakanin ‘yan uwa biyu

PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin ‘yan uwa biyu, wanda ake zargin ya afka dakinsa, tare da dauko bindiga ya harbe dan uwansa inda nan take ya ce ya ce ga garinku.
“Abinda ya faru shine tuntuni dama akwai ‘yar tsama tsakaninsu. Sun dade suna samun sabani a kan fili,” wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, a daren Alhamis.
Mista Ikenga, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce an kama wanda ake zargin.

“An fara kama matar wanda ake zargin a lokacin da abin ya faru daga baya kuma aka kama wanda ake zargin,” inji shi. “Dukansu suna hannunmu.”

Ya kara da cewa “Kwamishanan ‘yan sanda a jihar, Echeng Echeng, ya bada umarnin a mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike.


Yan sanda sun kama wani tsohon soja da yake safarar makamai ga ‘Yan ta’adda a jihar Zamfara

Jami’an ‘yan sanda a jihar Zamfara, sun kama wani tsohon soja kuma fitaccen dan fashi da ya ke kai wa ‘yan ta’adda makamai a yankin Arewa maso Yamma.

Wanda ake zargin, mai suna Sa’idu Lawal, an ce ya dade yana ta’addanci ga al’ummar jihohin Neja, Kaduna, Katsina, da kuma Kebbi.

Tsohon sojan yayi ritaya ne domin ci gaba da fasakwaurin makamai
Sa’idu Lawal, din wanda dan asalin jihar Zamfara ne, ya yi ritaya dan radin kansa daga aikin sojan Najeriya, a shekarar 2021, inda ya ci gaba da haramtacciyar sana’ar aikawa ‘yan fashi makamai, a yankin Arewa maso Yamma.
Sojojin sun kama shi ne a hanyar Kaduna zuwa Abuja, a lokacin da yake kan hanyarsa ta kai wa wani gungun ‘yan fashi da makami, makamai da suke addabar al’ummar karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, karkashin jagorancin Dogo Hamza.

Yayin da yake baje kolin da wanda ake zargin a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Mohammed Shehu, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan da rundunar ‘yan sanda ta (Tactical Squad) wato rundunar iya taku, da kuma tawagar ‘yan rakiya da ke aiki da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara suka samu bayanan sirri.

Yadda aka cafke mai laifin
A ranar 27 ga watan Agustan 2022 da misalin karfe 5:30 na yamma , rundunar ‘yan sandan da ke tare da tawagar kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Kolo Yusuf, sun kama wani mutum da ake zargin tsohon ma’aikaci ne, da ya taba aiki da Rundunar Sojojin Najeriya da ke Bataliya ta 73 dake barikin sojoji na Janguza a garin Kano.

An kama wanda ake zargin ne da wata mota kirar (Pontiac Vibe) mai lamba KRD 686 CY Lagos, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa jihar Zamfara. An gudanar da bincike a wurin, inda take kuma aka gano abubuwan da aka ambata a sama a hannunsa.”
Shehun ya ci gaba da cewa, A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa zai kai kayayyakin wurin baje koli, daga karamar hukumar Loko ta jihar Nasarawa, ga wani abokin cinikinsa wai shi Dogo Hamza, na kauyen Bacha a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa
Sa’idu, wanda ya amsa laifinsa, ya ce an kama shi ne a hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da yake jigilar bindigogi kirar AK-47 guda biyu da sauran alburusai, daga jihar Nasarawa zuwa jihar Zamfara.

Dangane da abin da yake samu a haramtacciyar harkallar tasa kuwa, ya ce ana biyansa Naira 200,000 a duk wata jigila da yayi, kuma ya karbi Naira 300,000 daga hannun wanda ya yi masa aiki.
An kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, hannun harsashi takwas, da harsashi mai rai 501, da kuma motar Pontiac a hannun mai laifin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe