27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tonon silili: Yadda Kwankwaso ya ci amana ta -Shekarau

LabaraiTonon silili: Yadda Kwankwaso ya ci amana ta -Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana dalilin da yasa ya fice daga jam’iyya mai kayan marmari (NNPP) ya koma jam’iyyar PDP.

Shekarau yace Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi masa shigo-shigo ba zurfi inda yaci amanar sa da shi da magoya bayansa a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ambato cewa Shekarau ya bayyana hakan ne a yayin wata hira a gidan talabijin na Channels TV a shirin su na Siyasa a yau.

Kwankwaso ya ƙi mutunta yarjejeniyar da suka yi

Yace jagoran na Kwankwasiyga da gangan ya ƙi aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma ƙafin ya koma jam’iyyar har zuwa lokacin da INEC ta dai na amsar sunayen ƴan takara.

Mun miƙa mu su buƙatun mu, da ni da dukkanin magoya baya na da abokanan siyasa ta, sannan muka zauna da Rabiu Kwankwaso. Na miƙa masa buƙatu na kuma ya amince da su. Yace a cikin kwana ɗaya ko uku zai yi nasa daga nan zamu zauna da shi mu duba mu ga abinda zamu iya yiwa ƴan takarar daga mazaɓu daban-daban.

Ina ganin cewa ba wani babban abu bane mu zauna mu shirya ƴan takara daga ɓangaren sa da nawa. Mun yi ta jira. Na miƙa masa sunaye a ranar 10 ga watan Mayu sannan na sake tuna masa a ranar 11 ga watan Mayu. A lokacin ni da mutane na mun gama yanke shawara.

Yadda aka ci amanar Shekarau

Shekarau ya kuma ƙara da cewa yayi matuƙar mamaki da ya ga sunayen da jam’iyyar ta fitar na ƴan takara an rubuta su da hannu.

Mun gaya musu cewa sam ba zamu yarda da hakan ba, saboda a gabaɗaya cikin sunayen, suna ne kaɗai ya fito daga ɓangare na.

Abinda ya bamu mamaki, kwana biyu daganan, ɗan’uwan Rabiu Kwankwaso ya tattauna da BBC Hausa, inda yake cewa ba yadda za a yi a biya mana buƙatun mu saboda mun shiga jam’iyyar a makare. Jam’iyyar da muka shiga lokacin da ake tantance ƴan takara ana zaɓen fidda gwani?

Abinda kawai za a kira hakan da shi cin amana, rashin ganin mutuncin mu da maguɗi. Manufar da muka sanya a gaba itace kare mutuncin mu.

Kwankwaso ya fasa kwai, ya bayyana abinda NNPP ta kasa yiwa Shekarau

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin da yasa jam’iyyar ta kasa cika wata alfarma da ƴan ɓangaren tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, suka yi.

Ya kuma ce ba wani saɓani a tsakanin shi da Shekarau, ɗan takarar sanata na Kano ta tsakiya a jam’iyyar

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe