27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tallafin kudin mai:’Yan majalisar Wakilai sun fara tantance yawan man da ake amfani da shi a kullum a Najeriya

LabaraiTallafin kudin mai:'Yan majalisar Wakilai sun fara tantance yawan man da ake amfani da shi a kullum a Najeriya
Petrol

Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan harkokin da suka shafi amfani da man fetur sun fara tantance yawan man fetur din da ake amfani da shi a kullum.

Shugaban kwamitin, Uzoma Abonta,wanda ya jagoranci sauran mambobin kwamitin a ziyararsgani da ido a gidajen mai da ke garin Calaba.

George Ene-Ita, kodinetan na, Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority, ofishin shiyyar Kudu shi ne ya jagoranci zagayen gonakin man.
Mista Abonta ya ce bisa la’akari da muhawarar da ake yi kan ko ya kamata a cire tallafin man fetur ko a’a, majalisar wakilai ta kafa kwamitin da zai yi dubi da yadda ake amfani da mai a kasar.

A cewarsa rahoton kwamitin majalisa za ta yi amfani da shi a matsayin sheda domin kamala batutuwan da suka shafi tallafin.

“Muna kokarin gano yawan mai da ake amfani da sh a kasar a kullum. Majalisar wakilai za ta yi amfani da wannan rahoto a matsayin sheda don kammala wasu bincike.
Tallafin ya zama batun da ya dade yana ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya sai dai ba za a iya samun asalin kididdigar lissafin tallafin ba tare da sanin ainihin yawan shi ba.

“A karshen atisayen, idan mun sami lissfin daidai, Majalisar Wakilai ita ya dace ta jagoranci wannan batu tare da dubi akan tallafin yadda ya kamata ko kuma ta yi wani abu.

An yi ta cece-kuce kan batun tallafi; musamman kan wanda ya biya , wanda ya samu da kuma daraja” ya kara da cewa.

Wasu daga cikin gidajen tankunan da aka ziyarta sun hada da, Northwest Petroleum, Ammasco Petrochemicals Company, Mainland Oil and Gas, Alkanes, Sobaz, Ibafon da Blokks.

Yan sanda sun sha alwashin kama masu fasahar kera lambobin mota ba bisa ka’ida ba

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sha alwashin bin diddigin masu kera sabuwar fasahar da ke bai wa masu motoci damar sauya lambobi ba tare da izini ba.

Mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi, wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a ranar Talata, inda ya tofa albarkaci bakinsa ga wannan sabuwar dabarar.

‘yan Najeriya su guji wannan dabarar

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan hanya, inda ya kara da cewa kowace mota tana da hakkin mallakar lamba daya ne kacal.

Martanin nasa ya biyo bayan wani faifan bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta inda aka ga wata mota na amfani da wannan sabon salon mallakar lambar mota.
Motar mai dauke da lambar sirri hade da na fadar shugaban kasa, an gan ta tana sauya faifan lamban kai tsaye.

‘yan Najeriya sun maida martani

Tuni dai ‘yan Najeriya suka mayar da martani kan faifan bidiyon inda da dama suka yi tsokaci inda wasu ke kara nuna cewa wannan fasaha ce da bata gari ka iya amfani da ita.
A guji wannan fasahar
Da yake mayar da martani game da sabon tsarin, Mista Adejobi, wanda shi ma ya yada bidiyon, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da fasahar, ya kara da cewa yana da hadari da kuma illa ga tsaron kasa.

Za a dau mataki
Ya ce rundunar ‘yan sandan za ta hada kai da hukumomin da abin ya shafa domin dakile wuce gona da iri da masu motoci ke yi dangane da lasisin lambar mota.
Jawabin Jami’an tsaro

“Mun ga wannan bidiyon tabbas Wannan fasaha ce mai kyau amma sai dai tana da hadari a al’amuranmu na Najeriya kuma ya kamata a yi Allah wadai da ita.

“Kowace mota a Najeriya dole ne a yi rajista kuma lamba daya kawai aka yadda ta mallaka.

“Za mu yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa a wannan fanni domin dakile yaduwa da kuma amfani da lambobi na jabu .

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe