27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Yan sanda sun chafke wani mutumi da laifin sace motar Ubangidansa don biyan kudin jirgi zuwa kasar waje

LabaraiYan sanda sun chafke wani mutumi da laifin sace motar Ubangidansa don biyan kudin jirgi zuwa kasar waje
Fyaɗe

Rundunar ‘yan sanda a Legas ta kama wani matashi dan shekara 21 mai suna Temple Samuel da laifin sata tare da siyar da motar ubangidansa Lexus ES 330 a unguwar Ogba da ke jihar.

yan sanda sun tabbatar da faruwan lamari

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a jihar ta Legas.

Ya ce jami’an ‘yan sandan Legas Rapid Response Squad (RRS) ne suka kama wanda ake zargin tare da abokan sa su uku.

“An kama Samuel ne a yankin Ogba na jihar tare da wasu mutane uku: Benjamin Bassey,mai shekaru 32; Chukwuemeka Okorie mai shekaru, 29; da Joshua Agboche, mai shekaru 37, wanda suka hada baki da shi wajen sayar da motar.

Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin yana aiki a gida wankin mota maigidan nasa a Egbeda inda ya gudu da motar dauke da wayan maigidan sa iPhone X da iPhone 13 zuwa gidan Bassey da ke Ikeja da tsakar dare.
Haka kuma ya cire kudi kimanin N75,000 daga asusun bankin maigidansa,” cewar dan sanda.
Kakakin ‘yan sandan ya ce Mista Samuel ya sayar da motar ne da nufin yin amfani da kudaden don ya tsallake zuwa kasar waje .

Wanda ake zargin ya kammala shirye-shiryen yin amfani da kudaden da aka samu na siyar da motar da sauran kayayyaki masu tsada da ya sata don tafiyarsa zuwa kasar waje,” in ji shi.

An bada umurnin mika mai laifi zuwa kotu

Mista Hundeyin ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Abiodun Alabi, ya bayar da umarnin a mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID), Panti, domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da mai laifin gaban kuliya.

Yan sanda sun kama wani tsohon soja da yake safarar makamai ga ‘Yan ta’adda a jihar Zamfara

Jami’an ‘yan sanda a jihar Zamfara, sun kama wani tsohon soja kuma fitaccen dan fashi da ya ke kai wa ‘yan ta’adda makamai a yankin Arewa maso Yamma.

Wanda ake zargin, mai suna Sa’idu Lawal, an ce ya dade yana ta’addanci ga al’ummar jihohin Neja, Kaduna, Katsina, da kuma Kebbi.

Tsohon sojan yayi ritaya ne domin ci gaba da fasakwaurin makamai
Sa’idu Lawal, din wanda dan asalin jihar Zamfara ne, ya yi ritaya dan radin kansa daga aikin sojan Najeriya, a shekarar 2021, inda ya ci gaba da haramtacciyar sana’ar aikawa ‘yan fashi makamai, a yankin Arewa maso Yamma.
Sojojin sun kama shi ne a hanyar Kaduna zuwa Abuja, a lokacin da yake kan hanyarsa ta kai wa wani gungun ‘yan fashi da makami, makamai da suke addabar al’ummar karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, karkashin jagorancin Dogo Hamza.

Yayin da yake baje kolin da wanda ake zargin a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Mohammed Shehu, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan da rundunar ‘yan sanda ta (Tactical Squad) wato rundunar iya taku, da kuma tawagar ‘yan rakiya da ke aiki da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara suka samu bayanan sirri.

Yadda aka cafke mai laifin
A ranar 27 ga watan Agustan 2022 da misalin karfe 5:30 na yamma , rundunar ‘yan sandan da ke tare da tawagar kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Kolo Yusuf, sun kama wani mutum da ake zargin tsohon ma’aikaci ne, da ya taba aiki da Rundunar Sojojin Najeriya da ke Bataliya ta 73 dake barikin sojoji na Janguza a garin Kano.

An kama wanda ake zargin ne da wata mota kirar (Pontiac Vibe) mai lamba KRD 686 CY Lagos, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa jihar Zamfara. An gudanar da bincike a wurin, inda take kuma aka gano abubuwan da aka ambata a sama a hannunsa.”

Shehun ya ci gaba da cewa, A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa zai kai kayayyakin wurin baje koli, daga karamar hukumar Loko ta jihar Nasarawa, ga wani abokin cinikinsa wai shi Dogo Hamza, na kauyen Bacha a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa
Sa’idu, wanda ya amsa laifinsa, ya ce an kama shi ne a hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da yake jigilar bindigogi kirar AK-47 guda biyu da sauran alburusai, daga jihar Nasarawa zuwa jihar Zamfara.

Dangane da abin da yake samu a haramtacciyar harkallar tasa kuwa, ya ce ana biyansa Naira 200,000 a duk wata jigila da yayi, kuma ya karbi Naira 300,000 daga hannun wanda ya yi masa aiki.

An kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, hannun harsashi takwas, da harsashi mai rai 501, da kuma motar Pontiac a hannun mai laifin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe