28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Bakar hassada ta tunzura matashi halaka abokinsa bayan ganin ya siya dalleliyar mota

LabaraiBakar hassada ta tunzura matashi halaka abokinsa bayan ganin ya siya dalleliyar mota


Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta samu nasarar kama wani mutum bayan ya halaka abokinsa tare da birne gawarsa a gidansa da ke Lokoja, Jihar Kogi.

Bisa ruwayar LIB, lamarin ya auku ne a wuraren Felele da ke Lokoja inda mamacin ke zama da iyalinsa.

An tattaro rahotanni dangane da yadda Kehinde Ajayi, wanda aka halaka, ya samu nasarar siyan mota kirar Toyota Sienna mai kalar ruwan toka a ranar 24 ga watan Yulin 2022.

Sai dai abokinsa yana aikin gyaran na’urar sanyaya wuri ne. Kuma hassada ta sanya shi jan Kehinde zuwa wani wuri da misalin karfe 10 na safiyar ranar da sunan zai taya shi murnar siyan motar.

Majiyoyi sun nuna yadda mutumin ya ja Kehinde da wani zuwa wurin, kuma tun daga nan ba a sake jin duriyarsa ba.

Bayan ganin ba a ga Kehinde bane wasu ‘yan uwansa su ka kai rahoto ofishin ‘yan sanda daga nan aka kama wanda ake zargin yana da alhakin satarsa.

Anan ne ya tabbatar musu da cewa ya halaka shi sannan ya sace motarsa. A ranar Litinin, 29 ga watan Augusta ya kai ‘yan sanda gidansa inda ya birne gawar Kehinde.

An samu bayani akan yadda wasu matasa su ka kai farmaki gidan mutumin bayan ganin ‘yan sanda sun fito da gawar Kehinde.

SP William Ayah, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace su na ci gaba da bincike don bankado wadanda su ka taya shi aiwatar da mummunan lamarin.

Hotuna: Abba Kyari tauraron dan sanda da mashahuran mutane ke hassada da shafinsa na Instagram

Kafin yanzu, sunan DCP Abba Kyari ya zama abin sha’awa da mutuntawa tsakanin ‘yan Najeriya, kuma sunan na sanya fargaba da tsoro a zuciyar masu cin amanar kasa, amma a cikin awanni 24, an alakanta sunanshi dana ‘yan damfara, sakamakon wani zargi da kotun Amurka ke yi akan shi kan damfarar fitaccen dan damfara Hushpuppi.

Hushpuppi, wanda ainahin sunanshi shine Ramon Abbas, ya bayyana cewa ya bawa Abba Kyari cin hanci, ya kama abokin harkar shi.

Sai dai kuma, fitaccen dan sandan ya karyata wannan zargi da Hushpuppi yake yi akan shi, inda ya ce bai karbi ko kobo daga wajen shi ba.

Jaridar Labarun Hausa ta ruwaito cewa kotun kasar Amurka ta bawa hukumar FBI umarnin kamo Abba Kyari biyo bayan zargin shi da ake da hannu a badakalar Hushpuppi.

Sai dai kumaa, a wani rahoto mai alaka da wannan din, Sufeto Janar, Usman Alkali Baba, ya bukaci a gabatar da bincike akan zargin da ake yiwa Abba Kyari.

Kyari dai yana da masoya 73,000 a shafinsa na Instagram a daidai lokacin da muke rubuta wannan rahoto, kuma mutane da dama na son mu’amala da shi.

Daga wallafa irin nasarorin da yake samu, zuwa wallafa hotunan abokanan shi da ‘yan uwanshi, Kyari yana wallafa kusan duk abubuwan da yake yi na rayuwa a shafinsa na Instagram.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe