27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

An kama ma’aikacin lafiyar da ya dage rigar mara lafiya don daukar hoton albarkatun kirjinta

LabaraiAn kama ma’aikacin lafiyar da ya dage rigar mara lafiya don daukar hoton albarkatun kirjinta


Wani ma’aikacin lafiya da ke yankin Delaware yana fuskantar tuhuma dangane da yadda ya bude tsiraicin mara lafiya wacce take a mawuyacin yanayi don daukar hotunan albarkatun kirjinta, LIB ta ruwaito.

Kevin Hakeem Pressley mai shekaru 24 ma’aikacin Brookhaven Fire Co. Ambulance ne, kuma an kama shi ne a ranar Asabar, 27 ga watan Augusta akan dage rigar maman mara lafiya don daukar hotunan tsiraicinta a bayan motar kawo dauki.

Kamar yadda ‘yan sanda su ka bayyana ranar Litinin, 29 ga watan Augusta, Pressley yana daya daga cikin ma’aikatan lafiya masu kawo taimakon gaggawa, kuma an bukaci ya tallafawa matar wacce take fama da ciwon kirji.

An bukaci ya wuce da ita daga Brookhaven zuwa asibitin Crozer Chester da misalin karfe 6:30 na yammacin Alhamis, 25 ga watan Augusta, kamar yadda ‘yan sanda su ka shaida.

Yayin da su ke kan hanya, ana zargin Pressley da aka bari da matar a bayan motar, da bayyana tsiraicinta sannan ya dauki hotunanta yayin da take a mawuyacin yanayi.

Ana zarginsa da rashin kamun kai, bayyana tsiraici, tozarci da rashin daraja. An bayar da belinsa a $100,000 kuma an sakaya shi ne a gidan gyaran halin George W. Hill da ke Glen Mills.

Masu bincike sun gano cewa ya taba aiki da wasu ma’aikatan lafiyar, don haka ‘yan sandan Brookhaven su na neman bayani idan akwai wacce ya taba cutarwa ta sanar da su yadda su ka yi.

Abin al’ajabi: Ma’aikatan lafiya 11 a wani asibiti sun samu juna biyu a tare, 2 daga ciki rana ɗaya za su haihu

Ma’aikatan lafiya mutum 11 masu aiki a wani asibitin birnin Missouri, suna ɗauke da juna biyu a lokaci ɗaya, inda biyu daga cikin ma’aikatan jinya daga cikin su, ake sa ran haihuwar su a rana ɗaya. Shafin LIB ya rshoto

A asibitin Liberty Hospital cikin Liberty, birnin Missouri, ma’aikatan jinya 10 da wata likita guda ɗaya suna ɗauke da juna biyu inda ake sa ran haihuwar su cikin watanni masu zuwa.

Da dama daga cikin su aiki ne a ɓangare guda

Da yawa daga cikin ma’aikatan lafiyan masu ɗauke da juna biyun, suna aiki ne a sashin unguwar zoma da kuma karɓar haihuwa.

Darektan ɓangaren karɓar haihuwa, Nicki Kolling ya shaida wa Fox4 KC cewa:

Koda yaushe suna yin abubuwan su rukuni-rukuni, amma ba mu taɓa samun guda 10 a lokaci ɗaya ba, saboda haka wannan abin raha ne.

Ko a baya an taɓa samun irin haka

Wannan dai ba shine karon farko ba da wani asibiti ya samu ma’aikatan sa da dama na ɗauke da juna biyu a lokaci daya ba.

A shekarar 2019, ma’aikatan jinya 9 masu aiki a ɓangaren karɓar haihuwa a asibitin Maine Medical Center, suna ɗauke da juna biyu a lokaci ɗaya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe