29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Yadda aka tsinci gawar daliban jami’a, mace da namiji tsirara a dakinsu da ke wajen makarantar

IlimiYadda aka tsinci gawar daliban jami’a, mace da namiji tsirara a dakinsu da ke wajen makarantar


Dalibai guda biyu na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Malete sun sheka lahira a dakinsu da ke wajen makarantar. Abokan karatun Tobiloba Daniel da Arewa Abayomi ne su ka tsince su a mummunan yanayin, LIB ta ruwaito.

Dukkansu aji biyu su ke a jami’ar kuma a dakin Daniel ne aka tsinci gawar. Wani dalibin jami’ar KWASU ya sanar da manema labarai cewa:

“Dama muna zargin soyayya su ke yi. Hankula sun tashi ne bayan mun kula da cewa ba ma ganinsu lokacin jarabawa na tsawon kwana uku.

“Sai wasu abokansu su ka je dakinsu da ke wajen makaranta inda su ka ga gawarsu tsirara. Mun fi zargin guba su ka sha.”

Sai dai Kakakin KWASU, Hajia Saeedat Aliyu, ta ce ba su da masaniya dangane da lamarin don har yanzu babu wanda ya sanar da su.

Amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya kara da cewa:

“Mun samu labari akan yadda aka tsinci gawarsu a cikin dakinsu. Hakan yasa ‘yan sanda su ka garzaya har wurin.

“Jami’anmu sun balle kofar sannan su ka zarce da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH) don bincike. Yanzu haka ana kan binciko dalilin mutuwarsu.”

Kotu a Birnin Karnataka na kasar India ta hana dalibai mata sanya Hijabi a Makaranta

Yayin da Musulman Indiya ke tsaka da damuwa game da matakin ‘Hindu na farko’ da gwamnati ta yi, babbar kotun jihar Karnataka ta kasar Indiya ta kara dagula al’amura inda ta bayyana cewa ta amince a hukumance ta tabbatar da dokar hana sanya hijabi ga dalibai musulmi a makarantu.

Kotun ta ce hijabi ba wani muhimmin aikin addini ba ne a Musulunci. Don haka ba za a ba shi kariya daga sashe na 25 na kundin tsarin mulkin kasar ba, kundin da yake magana akan ‘yancin yin addini. Kotun ta kuma ce ‘yancin da jihar ke da shi na yanke hukuncin abin da dalibai za suyi ya kasance mai mutunci ne kawai.

A baya an samu barkewar rikicin sanya hijabi a wata makarantar Kwaleji

A watan Satumbar Shekarar 2021 ne rikici ya barke a wata makarantar mata ta gwamnati da ke Udupi, Karnataka, inda aka hana dalibai musulmi shiga ajujuwa saboda suna sanye da hijabi. A cewar kwalejin, saka hijabi abu ne da ake daukarsa a matsayin keta dokokin makarantar.

Dalibai sun yi zanga akan an tauye musu hakki

Abu kamar wasa yazo ya zama abin cece-kuce, har ta kai dalibai musulmai sun yi zanga-zangar cewa an tauye musu hakkinsu na yin addininsu saboda wannan doka, inda dali suka ce a baya sun kasance suna sanya hijabi a makaranta ba tare da wata matsala ba.
Lamarin ya harzuka mutane a duk fadin Indiya da kewaye inda abun ya zama babbar tambaya a tsakanin jama’a. Ba wai batun hijabi kadai ba, yawancin mutane a Indiya suna sanya tufafi na musamman saboda addininin su. Amma kamar rikicin ya fi karfi tsakanin Musulmai da Hindu a Indiya.

Kundin tsari ya ba da ‘yancin addini
Ba a kafa kasar Indiya bisa addini ba. A matsayin shaida, kundin tsarin mulkin Indiya ya kare ‘yancin yin addini. Sai dai hakan ya bambanta da abin da ake yi da Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi da jam’iyyarsa ta siyasa, BJP (Bharatiya Janata Party).
Ya yi kokari matuka wajen ganin ya sanya bukatun mabiya addinin Hindu kusan kashi 80 sama da bukatun sauran tsirarun addinai, musamman kashi 14% na al’ummar musulmi da ke kasar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe