29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Yadda na hadu da mijin da na aura a Otal din da na raka saurayina lokacin ina budurwa, Matar aure

LabaraiYadda na hadu da mijin da na aura a Otal din da na raka saurayina lokacin ina budurwa, Matar aure


Wata mata ta bayyana yadda su ka hadu da mijin da ya aureta yayin da ta fita shakatawa tare da tsohon saurayinta a shafint na Facebook , LIB ta ruwaito.

Matar mai suna Millicent Nwanyimarania ta bayyana yadda ta hadu da mijin a shekarar 2016 yayin da ta raka saurayinta otal don amsar wasu takardu.

A cewarta ta tsaya gefen wurin wanka ne tana jiransa kawai sai ta hango wani hadaddan saurayi ya tunkarota. Tun a lokacin ta ji ta fada tarkon soyayyarsa.

Ta ci gaba da cewa:

“Ya fara da tambayata yadda nake tare da tambayar idan ina tare da wani ne. Ni kuma na shaida masa cewa na raka wani dan uwana ne wanda yaje ganin wani.”

Ta shaida yadda su ka tsinke da hira har yana sanar da ita daga garin da yake ita ma ta shaida masa nata garin. Ta ce duk ta kosa ya amshi lambarta.

Ta ci gaba da cewa:

“Muna musayar lamba sai saurayina ya fito mu ka tafi. Mutumin nan ya kwashe tsawon lokaci bai kirani ba har kawayena su na zolayata akan cewa kila ma ko ajiye lambata be yi ba.”

Ta ce bayan wata daya ne mutumin ya kira ta inda ya shaida mata cewa tafiya yayi shiyasa be kirata ba.

“In takaice muku bayani dai mun ci gaba da soyayya har mu ka yi aure a shekarar 2020 a watan Nuwamba. Yanzu haka muna da diya kyakkyawa guda daya,” a cewarta.

Sai dai ta ce kada mutane su caccaketa don bata san abinda ya ja ra’ayinta ba, kila Ubangiji ya so sadata da mijinta ne ta hanyar saurayinta.

Ta yi karya ne saboda ta hadu da mutum mai cikakkiyar kamala da siffa.

Yadda dattijo mai shekaru 65 ya sheka lahira yana tsaka da gwada kwazonsa da budurwa a otal

Wani labari mai firgitarwa ya auku a garin Akwa da ke Jihar Anambra wanda wani dattijo mai shekaru 65 ya sheka lahira yayin da ya ke tsaka da lalata da wata Odion Ekeinde, budurwarsa a wani otal ranar Asabar, Amihad ta ruwaito.

Mutumin mai suna obi Nwoda ya kebe da budurwar ne a mai shekaru 34 a wani katafaren otal inda su ma dinga sheke ayarsu yadda su ka ga dama.

Jami’an tsaro sun garzaya da gawarsa zuwa wani babban asibiti da ke jihar inda likitoci su ka tabbatar da mutuwarsa.

Wani babban jami’in rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Haruna ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin inda yace akwai ayar tambaya dangane da mutuwar dattijon.

Rahotanni sun bayyana cewa bai riga ya cika ba a lokacin da aka matar ta razana ta nufi asibiti da shi. Sai dai yayin da ta ke kokarin kai shi ne lokacinsa da yayi.

DPO Haruna ya tabbatar da cewa akwai lauje cikin nadi dangane da mutuwar dattijon kuma jami’ansa sun yi ram da budurwar inda su ke ci gaba da bincike.

Sai dai budurwar ta tabbatar da cewa dattijon na tsaka da nuna mata kokarinsa akan gado ya fita daga hayyacinsa. Gawar dattijon tana asibiti yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike akan budurwar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe