Alamu sun nuna cewa mambobin Kungiyar malaman jami’a, ASUU sun tafi yajin aikin sai bata ta gani baya ganin gwamnatin tarayya ta ki biya musu bukatunsu, Daily Trust ta ruwaito.
An gano yadda lakcarori su ka zartar da wannan mataki yayin taron shugabannin Kungiyar na kasa, wanda aka fara da misalin karfe 12:15 na daren Litinin har sai da su ka yi awanni 4 su na yi a ofishin ASUU da ke jami’ar Abuja.
Basu riga sun saki wata takarda ba dangane da taron da suka yi, amma akwai majiyoyi masu karfi da su ka tabbatar da cewa yawancin jami’o’in da aka zauna da su sun nuna sun amince aje yajin aikin sai baba ta gani.
An gano cewa baya da hakan, wasu malaman sun bukaci kungiyar ta dena zama da gwamnatin tarayya har sai an kafa wata gwamnatin ranar 29 ga watan Mayun 2023.
ASUU ta bayyana batun tafiya yajin aikin a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kuma an ci gaba yajin na tsawon watanni 6.
Majiyar Daily Trust wacce ta kai ziyara jami’ar Abuja a ranar Lahadi, wani mamban ASUU ya ce am dakatar da manema labarai daga daukar taron kungiyar.
Sai dai wani mamban NEC din ASUU ya shaida wa Daily Trust cewa tabbas ba za su kara sauraron gwamnatin tarayya ba har sai an kafa sabuwar gwamnati.
Yayin da aka tambaye shi dalilin hakan ya ki bayani mai tsawo.
Yajin aikin ASUU: Yadda dalibin jami’a ya ragargaje kan kishiyar mamarsa da tabarya
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta yi ram da matashi mai shekaru 25, Najib Umar Shehu wanda ya lakada wa kishiyar babarsa duka da tabarya har sai da ta rasa ranta, LIB ta ruwaito.
Dalibin da ke aji na biyu ne Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma ya dade yana samun rashin jituwa da kishiyar mamarsa, Asiya Mohammed wacce tsohuwar ma’aikaciyar gwamnatin Jihar Katsina ce, har yana yawan ikirarin zai kashe ta.
Kakakin rundunar, SP Gambo Isah a wata takarda da ya saki a ranar Alhamis, 25 ga watan Augusta ya bayyana yadda matashin ya karya kafar mahaifinsa da tabaryar.
“A ranar 18 ga watan Augustan 2022, da misalin karfe 4 na yamma, Najib Shehu, mai shekaru 25 da ke Ambassador Quarters a Katsina ya samu sa-in-sa da kishiyar mamarsa, Asiya Mohammed mai shekaru 60.
“Nan da nan ya nufi kicin inda ya dauki tabarya ya dinga rotsa mata a kanta har sai da ta ji raunuka da dama inda daga bisani likita ya tabbatar da mutuwarta.
“A wurin ne ya dinga buga wa mahaifinsa tabaryar a kafa har sai da ya kakkarye a wurare daban-daban. Yanzu haka an kama wanda ake zargin wanda ya amsa laifukansa.
“An kwace tabaryar daga hannunsa kuma ana ci gaba da bincike,” kamar yadda takardar ‘yan sanda tazo.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: @labarunhausaagmail-com