29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Na yi nadamar sauya halitta ta, Wata mata ta kokan kan yadda labbanta ke ta kara girma

LabaraiNa yi nadamar sauya halitta ta, Wata mata ta kokan kan yadda labbanta ke ta kara girma

Wata mata wacce ta so mayar da lebenta kamar yadda take a baya, bayan biyan likita makudan kudade don ya sauya mata shi tana fama bayan lebenta ya koma tamkar balam-balan, LIB ta ruwaito.

Karli Gardner ta ce sai da tayi gwaje-gwajen asibiti wanda ya nuna mata babu wata matsala don ta yi gyaran a lebanta, hakan ya bata damar amincewa da likita yayi mata aikin.

Sai dai tana fama don tun da aka yi aikin labbanta su ka ci gaba da girma tamkar ana hura su.

Yayin da take bayyana halin da take ciki a TikTok, Karli ta ce ta ci gaba da gyaran duk da dai bata ji dadin yadda labbanta su ka yi manya ba bayan kammala aikin.

A cewarta:

“Ina nan ina fama da kai na, na yi gwaje-gwaje a asibiti kuma an ga cewa babu wata matsala, amma ga halin da nake ciki yanzu.”

Ta ci gaba da cewa:

“Wannan ma aya ce ga masu son kara girman labbansu.”

Cike da hawaye Karli tace ba ta son yadda su ka koma duk da bayan an kara mata girmansu ta yi kokarin mayar da su yadda suke a baya amma sai ci gaba suke yi da girma.

Wani mutum mai suna Amos ya bayyana cewa duk da kankantar halittar sa Ubangiji yayi masa Baiwar auren kyakyawar Mace

Sabanin yadda mutane da yawa zasu dubi lamarin ta wata fuska, wani karamin mutum Najeriya mai suna Efuoma Amos, ya ce a ko da yaushe samun budurwa baya masa wahala. Amos wanda ya zama babban maudu’i da aka yi ta tattaunawa a kafafen yanar gizo bayan da hotunansa tare da doguwar matarsa suka bayyana.Sannan a wata hira da BBC ta yi dashi ya shaida wa BBc cewa a gaskiya Allah ya ba shi farin jinin ‘yan mata.
Amos ya bayyana cewa gaskia Allah ya bashi farin jinin ‘yan mata suna sonsa duk da cewa ba baya iya musu. Ya kara da cewa yana alfahari da yadda Allah ya yi masa baiwar farin jini wanda ko dogayen mazan ma basu kaishi ba .
Ga abinda yace:” Tun da aka haifeni samun mace bai taba bani wahala ba”
“Ko,dogayen maza basuda farin jinin da Allah ya yi min.
“Kawai haka nan Allah ke jarabtan su da kauna ta. “A shekarar da nayi bautan kasa a jihar Ebonyi duk wata kyakawar budurwa da ni take harka.”So na suke suna bi na, ba kuma wai dab kudi naba dan ni talaka ne”

Auren Amos a shekarar 2018

Amos ya ce ya yi auren sa na farko ne a shekarar 2018 amma auren bai wuce shekara biyu ba suka rabu saboda sabanin dasuka samu a tsakanin su .Ya kara da cewa mutane sun yi ta masa dariya wai ba zai kara aure ba saboda ya rasa abin da Allah Ya ba shi, sai ya basu ansa cewar ai basu suka halicce shi ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe