28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Yadda zakaran AFCON ya ki rike kwalbar giya yayin daukar hoto, ya ce haramun ne a Musulunci

LabaraiYadda zakaran AFCON ya ki rike kwalbar giya yayin daukar hoto, ya ce haramun ne a Musulunci


– Tauraron Senegal, Sadio Mane ya ki amincewa ya rike kwalbar giya a hoton da su ka dauka saboda musulunci ya haramta hakan

– Tauraron da abokan sana’arsa su na cikin wadanda su ka bayyana kulla sabuwar alaka da kamfanin giyar

– Sadio Mane musulmi ne wanda ba ya boye addininsa sannan ba ya shiga duk wasu harkokin da su ka jibanci giya

Sadio Mane ya ki yarda ya rike kwalbar giya a hoton kungiyar Bayern Munich wanda su ka yi kwanannan, Sport belief ta ruwaito.

Sai dai matashin ya dauki hoton ne tare da sauran abokan sana’ar bayan sun hada kai da wani kamfanin giya, Paulaner.

A hoton wanda aka watsa shi a kafafen sada zumunta, Mane da wani Noussair Mazraoui su ne kadai ‘yan wasan da su ka ki rike kwalbar Paulaner.

Hujjarsu kuwa ita ce saboda addininsu bai amince da giya ba don haramun ne ko taba ta. Mane da Mazraoui duk musulmai ne wadanda ba su yarda su sha giya ba saboda addininsu ya yi hana da hakan.

Sadio Mane ya shiga cikin zakakuran Jamus ne bayan ya samu nasarori shida daban-daban a kwallon da ya yi da Liverpool.

Zakaran AFCON din ya fara samun nasarori mabambanta bayan cin kwallo sau hudu a wasanni biyar da ya yi wa zakarun Jamus.

Hukumar Hisbah ta ƙona kwalaben giya na maƙudan kuɗaɗe a Jigawa

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta ƙona kwalaben giya sama da 5,550 wanda darajar kuɗin su takai N3.2m. 

Da yake magana bayan kammala aikin a ƙaramar hukumar Kazaure ta jihar, shugaban hukumar na jihar Jigawa, Ibrahim Dahiru, yace kayan mayen an kama su ne a zagayen da hukumar ke gudanarwa yanzu. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Ya bayyana adadin giyar da aka ƙwato

A cikin sati biyu mun ƙwace giya ta kai kwalabe 5,500 wanda kuɗin su yakai N3.2m. A cewar sa

Dahiru yace an gudanar da aikin ne bayan samun izni daga kotu wanda ya bayar da damar lalata giya.

Addinin musulunci ya hana shan giya d sauran kayan maye masu gusar da hankalin ɗan Adam, hakan yasa Hisbah ke ƙoƙarin tabbatar da kare lafiyar mutanen jihar nan.

A musulunci an haramta shan giya. Dokar jihar Jigawa ta haramta sha da cinikayyar giya.

Hukumar Hisbah zata ƙara zage damtse wurin hana shan giƴa

Dahiru yace hukumar zata cigaba wurin ƙara ƙaimi a faɗan da take da duk wani abun baɗala a jihar domin tabbatar da lafiya da jindaɗin mutanen jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar, Muhammad Muktar, wanda yana wurin lokacin da ake ƙona kwalaben, ya yabawa Hisbah bisa nasarar da suka samu na ƙwace kayan mayen.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe