23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Daga yin shiga irin ta musulmai kawai sai maza musulmai suke ta turo min sako wai zasu aureni – Inji wata matashiyar kirista

LabaraiDaga yin shiga irin ta musulmai kawai sai maza musulmai suke ta turo min sako wai zasu aureni - Inji wata matashiyar kirista

Wata matashiya, ta bayyana  yadda maza musulmai suka dinga tururuwar sakonni gareta, a shafin ta na tuwita,  suna neman ta yarda ta zama mata a garesu. 

Kamar yadda yawancin mutane suka sani, yana da sauƙi a gane addinin mutane ta yadda suke sanya tufafi. 

maza musulmai
Daga yin shiga irin ta musulmai kawai sai maza musulmai suke ta turo min sako wai zasu aureni 

Misali, kowa ya san cewa yawancin mata musulmi suna daura gyale a kawunansu. Da irin haka ce ta faru , inda wata mata ta janyo cece-kuce, bayan ta yada abin da ya  faru da ita, sakamakon sanya hoton ta a dandalin ta na tuwita, tana  sanye da dankwali kamar musulma .

Aikawa da sakon soyayya daga maza musulmai

 Ta bayyana  cewa,

“da yawan  mazajen musulmi sun yi ta aika mata da sakon cewa suna so ta zama matar su ta aure, a dalilin irin yadda shigar tata, ta burgesu, duk a zaton su ita musulma ce”.  

Bambancin ra’ayoyi akan wannan shiga

An sami ra’ayoyi mabanbanta da ga masu sharhi. Inda wasu suke cewa ya kamata matar ta daina yin shiga irin ta  musulmai tana nuna kamar Ita musulma ce,  domin hakan tamkar yaudara ce. 

A wani bangaren kuma, wasu kuma cewa suke yi,  ya kamata matar ta canza hoton da ta sanya a gurbin hoton shafin nata, domin kada musulmai su ci gaba da daukan cewa ita musulma ce.

Wata mata mai tsananin kyamar addinin Musulunci ta musulunta 

Wata likitar yara ‘yar asalin kasar Netherlands mai suna  Paulin, ta karbi addinin musulunci. 

Paulin din an  santa da kyamar addinin Musulunci inda aka jiyo ta tana cewa:

Paulin takan nemo bayanai akan musulunci kawai domin tayi batanci gareshi

“Na dade ina jin kiyayya ga addinin Musulunci, kuma ina bibiyar  dukkan kafafen yada labarai a kan duk abin da ya shafi addinin Musulunci, kuma ina karanta abubuwa game da musuluncin, inda nake samun bayanai da zan tattauna da mutane kawai domin in yi batanci ga addinin.” 

Bayan dogon nazari cikin tsanaki, sai na ji ina son wannan addini , sai na ga akwai abubuwan da suka dace da ni a matsayina na mutum, don haka nace a raina wallahi na tsani addinin musulunci,  amma akwai abubuwan da nake so a cikin sa. “

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

 

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe