27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Yadda kishi ya sanya wata matar aure ta yanke mazakutar mijinta

LabaraiYadda kishi ya sanya wata matar aure ta yanke mazakutar mijinta

Wata matar aure wacce tayi yunƙurin yanke mazakutar mijinta yayin da yake barci, ta samu hukuncin shekara uku a gidan gyaran hali. Lamarin dai ya auku ne a farkon wannan watan na Agusta, 2022.

Kotun da take yanke hukuncin ta saurari yadda mijin matar auren mai suna Jimmy Ngulube, wanda ya fito daga Kapiri Mposhi a ƙasar Zambia, ya farka cikin tsakar dare a ranar 4 ga watan Agusta, da sabon rauni a gaban sa. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Yadda lamarin ya auku

Ya ga matar sa mai suna Given Chilufya, tsaye a kan shi riƙe da wuƙa mai ɗauke da jini a jikinta tana barazanar halaka shi.

Tun da farko kafin su kwanta, Chilufya mai shekara 37 a duniya, ta zargi mijinta da neman mata a waje wanda hakan ya sanya rikici mai zafi ya ɓarke a tsakanin su.

Hakan ya sanya ta farka cikin tsakar dare domin ɗaukar fansa.

Jimmy mai shekara 43 a duniya, ya kira ɗan’uwan sa wanda ya tafi da shi zuwa asibiti inda likitoci suka samu suka gyara mummunan raunin da ya samu.

Cikin gaggawa aka sanar da jami’an ƴan sanda inda suka cafke matar auren.

Kotu ta samu matar auren da laifi dumu-dumu

A ranar 26 ga watan Agusta, alƙalin kotun majistare dake Kapiri Mposhi, Arnold Kasongamulilo ya yankewa Chilufya hukuncin shekara uku a gidan gyaran hali bisa yiwa mijinta rauni ba bisa ƙa’ida ba.

Chilufya ta roƙi kotun da tayi mata sassauci amma alƙalin ya haƙiƙance cewa yadda ta kai wa mijinta hari da yi masa rauni, ya nuna tana da niyyar halaka shi.

Yadda wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta kan yunkurin yiwa ƴar ta fƴaɗe

A wani labarin na daban kuma wata mata ta yankewa saurayinta mazakuta bisa yunƙurin yiwa ɗiyar ta fyaɗe.

Wata mata mai shekara 36 a duniya, ta yanke mazakutar saurayin ta mai shekara 32 a duniya, da wuƙa bisa zargin ƙoƙarin yiwa ɗiyarta mai shekara 14 a duniya fyaɗe.

Lamarin ya auku ne a yankin Lakhimpur Kheri, a jihar Uttar Pradesh ta ƙasar Indiya.

A cewar jami’ai, matar da ƴar ta suna rayuwa tare da mutumin na tsawon shekara 2 bayan ta rabu da tsohon mijinta mai shan giya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe