23 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

“Yadda ka ci amanata sai Allah yayi min sakayya” wani matashi ya caccaki Rarara

LabaraiKannywood"Yadda ka ci amanata sai Allah yayi min sakayya" wani matashi ya caccaki Rarara

Batun kyaututtukan gasar da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara, ya bayar na gasar da ya sanya ta Tinubu, ya bar baya da ƙura.

Wani matashi wanda ya shiga cikin gasar ya fito yayi ƙorafin cewa sam ba ayi masa adalci ba, inda yayi kalamai masu kaushi ga mawaƙin.

Rarara ya saka gasa kan waƙar sa ta Tinubu

Rarara dai ya sanya gasa ne a wata waƙa da yayi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, inda aka bayar da kyautar motoci, wayoyi da kuma kuɗaɗe ga mutanen da suka yi nasara.

Sai dai ba kowa bane yayi murna da hakan inda wannan matashin yana daga cikin su. Ya fito ya bayyana cewa sam mawaƙin bai musu adalci ba wurin zaɓar zakarun da suka yi nasara a gasar.

Matashin ya caccaki Rarara

Matashin wanda yayi magana a harzuƙe a cikin bidiyon ya bayyana cewa:

Abin akwai ɓacin rai, mun wahala wai ace abun bamu samu ba. Na rantse da Allah abun akwai ɓacin rai. Shin mu ba mu iya bane ko ba mu cancanta bane? Idan bamu cancanta bane to mu sani.

Yadda kaci amanata wallahi sai Allah yaci amanarka Rarara. Wallahi ban yafewa, yau cikin wani yanayi zan kwana, sai ka riga ni kwana cikin sa.

Mun zo mun kashe kuɗin mu mun wahala kai mugu wai kace bamu ci ba. Sai dai kayi Asiwajun nan kai kaɗai, ba zamu zaɓe shi ba.

Ga cikakken bidiyon nan ƙasa:

Bayan Rarara ya gwangwaje shi da N50,000, yayan Ado Gwanja ya ce ba ya bukata, kaskanci ne

A wani labarin na daban kuma, yayan Ado Gwanja ya mayar da kyautar N50,000 da Rarara yayi masa. Ya bayyana kyautar kuɗin da mawaƙin yayi masa a matsayin wani abun ƙasƙanci.

Yayan mawaki Ado Gwanja, Sa’idu Gwanja ya mayar da kyautar N50,000 da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi masa, inda ya ce ba ya bukata.

A wani bidiyonsa wanda Tashar Tsakar Gida ta wallafa, an ga inda Sa’idu ya ke bayyana hujjarsa ta kin amsar kudin

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe