34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Yadda wani ɗan ƙasar Ukraine ya musulunta bayan samun mafaka a masallaci yayin yaƙin Rasha-Ukraine

LabaraiYadda wani ɗan ƙasar Ukraine ya musulunta bayan samun mafaka a masallaci yayin yaƙin Rasha-Ukraine

Wani mutum musaki ɗan ƙasar Ukraine ya musulunta bayan ya samu mafaka a wani masallaci lokacin harin ƙasar Rasha.

Mutumin mai suna Voronko Urko, yayi kalmar shahada a ranar 20 ga watan Agusta, 2022. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Mutumin ya rasa gidansa da iyalansa

Kamar yadda TRT World ta rahoto, Urko ya rasa gidansa sannan an raba shi da matarsa da ƴaƴansa mata biyu kafin musuluntar sa. Daga nan sai Urko ya sami mafaka a wani masallaci cikin birnin Kharkiv, na ƙasar Ukraine.

Urko ya bayyana cewa an bar shi cikin kaɗaici bayan da masu bada agajin gaggawa suka tafi da iyalinsa zuwa wani wuri a ranar 8 ga watan Maris.

Urko ya cigaba da cewa duk lokacin da aka kawo hari, da shi da iyalansa suna samun mafaka su ɓoye. Sai dai, wanda aka bari a cikin hawa na 9 a wani gini, ya fara rayuwa cikin ƙunci saboda rashin iskar gas, wutar lantarki da ruwa.

Ya samu mafaƙa a masallaci

A cikin hakan ne taimako ya zo masa ta hannun wani limami mai suna Muhammad Ali, wanda ya bashi wuri a masallaci a birnin Kharkiv.

A cewar limami Muhammad Ali, Urko ya kira sannan ya nemi taimako lokacin d halin da yake ciki ya tsananta. Sai ya gayyace shi ya zo ya zauna masallacin, inda daga nan suka zama ƴan’uwa.

Bayan ya zauna a masallacin na wani ɗan lokaci, Voronko Urko ya samu shiriya inda ya rungumi addinin musulunci sannan yayi kalmar shahada a ranar 20 ga watan Agusta, 2022.

Wata mata mai tsananin kyamar addinin Musulunci ta musulunta 

A wani labarin na daban kuma, wata mata mai tsananin kyamatar musulunci ta musulunta. Matar wacce likita ce ta fannin yara, ta ka yi bincike akan musulunci domin samu abinda za ta aibata shi da shi.

Wata likitar yara ‘yar asalin kasar Netherlands mai suna  Paulin, ta karbi addinin musulunci. 

Paulin wacce aka santa da kyamar addinin Musulunci tace ta sha yin bincike da karance-karance domin samun bayanan da zata yi ɓatanci ga addinin musulunci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe