27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

“A Aljanna kuke, Buhari yafi shugaban ƙasar mu” Cewar wani ɗan ƙasar Kamaru ga ƴan Najeriya

Labarai"A Aljanna kuke, Buhari yafi shugaban ƙasar mu" Cewar wani ɗan ƙasar Kamaru ga ƴan Najeriya

Wani mutum ɗan ƙasar Kamaru a cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafin TikTok, ya nuna cewa gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tafi nesa ba kusa ba gwamnatin Paul Biya, shugaban ƙasar Kamaru.

Mutumin wanda yake magana cikin fushi a bidiyon, inda yake cewa mutanen ƙasar Kamaru sun rayu da wannan gwamnatin wacce bata taɓuka komai har na shekara 40. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Yana jin haushi idan yaji ƴan Najeriya na ƙorafi

Yace a duk lokacin da yaji ƴan Najeriya na ƙorafi, ya kan ji hakan a matsayin wani shirme a cikin kunnen sa, tunda suna cikin yanayi mai kyau fiye da ƴan ƙasar sa.

Shugaban ƙasa Paul Biya na ƙasar Kamaru, ya kasance a kan karagar mulki tun shekarar 1982, hakan ya sanya ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin da suka daɗe akan karagar mulki a nahiyar Afrika.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

Bori ya rubuta:

Shugaban ƙasar Equatorial Guinea shekarar sa 43, kuma har yanzu yana kan mulki.

@Nkirukamma Cherie Agusiobo ya rubuta:

Ɗan’uwa!!!!  A matsayina na ɗan Najeriya mun tausaya muku. Tabɗi shekara 40!!! Ku sarki gare ku ba shugaban ƙasa ba.

@user2332734943352 ya rubuta:

Najeriya shekara 8 ne kawai amma har jini na ya dai na yawo a jikina.

@Asamaowei Molly ya rubuta:

Da ace muna da irin wannan shugaban ƙasa wanda yayi shekara 40, da mun yi kisa  da yawa.

Ban taɓa ganin lusarin shugaban ƙasa irin Buhari ba -Salihu Tanko Yakasai

A wani labarin kuma Salihu Tanko Yakasai yace bai taɓa ganin lusarin shugaban ƙasa ba irin Buhari.

Ɗan takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Salihu Tanko Yakasai, ya yiwa shugaba Buhari wankin babban bargo kan yadda ya ƙyale mutanen da ya naɗa muƙamai ke ƙin bin umurnin sa ba tare da ya hukunta su ba.

Salihu Yakasai ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter bayan ƙarewar wa’adin sati biyu da shugaba Buhari yaba ministan ilmi, Adamu Adamu na tabbatar da cewa an kawo ƙarshen yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’a (ASUU) ke yi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe